Manyan jamíyun siyasar Jamus sun cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin gwiwa. | Labarai | DW | 15.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Manyan jamíyun siyasar Jamus sun cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin gwiwa.

Manyan jamíyun siyasar kasar Jamus sun amince da gagarumar rinjaye yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin gwiwa karkashin Jagorancin Angela Merkel. A babban tarukan da suka gudanar daban daban Jamíyun SPD da CDU tare da takwarar su ta CSU dukkanin su sun rattaba amincewa da daftarin yarejejniyar gwamnatin hadin gwiwar. An shafe tsawon wata guda ana tafka muhawara kafin a cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin gwiwar. A halin da ake ciki, a ranar 22 ga wannan watan ne majalisar dokokin jamus zata kada kuriár zabar Angela Merkel a matsayin sabuwar shugabar gwamnatin ta Jamus.