Manyan gasannin da za su gudana a 2023
Gasar kwallon kafar mata da wasannin motsa jiki na guje-guje da tsalle-tsalle na duniya da kwallon kwando da wasan kankara - kakar wasanni ta 2023 tana da wadatar abubuwa. Tuni ma aka farawa wasu.
Kofin kwallon hannu na duniya
Daga ranar 11 zuwa 29 ga watan Janairu, kungiyoyin kwallon hannu 32 da suka fi fice a duniya za su fafata a Poland da Sweden. Ba kamar yadda aka yi a Masar shekaru biyu da suka gabata ba, kungiyar Jamus za ta so sake kaiwa matakin wasan karshe don lashe gasar. Masu rike da kambun sune Denmark, wadanda suka doke Sweden a wasan karshe na 2021.
Gasar tsere kankara ta duniya
Daga 6 zuwa 19 ga Fabrairu, kwararrun 'yan tseren kankara za su fafata don samun lambobi na gasar cin kofin duniya a kan tsaunin Courchevel da Méribel na yankin Alps na kasar Faransa. Babban abun kallo daga Jamus shi ne Thomas Dreßen (hoto), wanda ya koma gasar cin kofin duniya bayan dogon rauni da ya yi, da kuma kwararriya Lena Dürr.
Gasar Super Bowl
A ranar 12 ga Fabrairu, za a gudanar taron wasanni mafi girma a duniya wanda zai gudana a Arizona na Amirka. Shi ne taron NFL karo na 57, kamar kullum, zai kasance mai girma - cikin tarukan motsa jiki. Abin da ya rage kawai ga magoya baya a cikin jihar hamadar Amirka: Cardinal Arizona, ita ce kungiya mai masaukin baki, mai yiwuwa ba za ta rasa wasannin share fage na wannan kakar ba.
Kwallon gora a kan kankara na duniya
Rasha, daya cikin kungiyoyin wasan kwallon gora na kan kankara masu karfi, ba sa halartan gasar a bana, da za a yi a Tampere na kasar Finland, da kuma Riga, babban birnin Latvia, a watan Mayu. Jamus na son yin fiye da yadda ta yi a 2022 lokacin da Jamhuriyar Chek ta fitar da ita a wasan kusa da na karshe (hoto). Sai dai kungiyar ta DEB na cikin rudani bayan da koci Toni Söderholm ya bar kungiyar.
Wasannin Olympics na musamman
Gasar Olympics ta musamman ita ce kungiyar motsa jiki mafi girma a duniya ga mutanen da ke da nakasar kwakwalwa. Za a yi wasannin bazara a Berlin a watan Yuni. Ita ce gasar Olympics ta musamman ta kasa da kasa ta farko a kasar Jamus. Ana sa ran kusan 'yan wasa 7000 daga kasashe 170 za su halarta. An riga an yi wasannin hunturu a watan Janairu a Bad Tölz a jihar Bavaria.
Tseren keke na Tour de France
Gasar tseren keke karo na 110 ta duniya za ta fara a 1 ga watan Yuli a Bilbao da ke arewacin Spain, kuma bisa ga al'ada za a kare ranar 23 ga Yuli a Champs-Élysées a birnin Paris. Abin daukar hankali a 2023 zai zama gagaran badau: a kan hanyar mai tsawon kilomita 3404, masu tseren keken za su haye nau'ukan tsauni har 30 a cikin mafi girman nau'ikan - don zama sabon zakaran tseren keke.
Gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya
Gasar cin kofin kwallo kafan duniya ta mata ba ta taba yin irin wannan ba: Daga ranar 20 ga watan Yuli zuwa 20 ga Agusta, kungiyoyi 32 ne za su halarci gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a Ostiraliya da New Zealand a karon farko. Tawagar Jamus na son sake samun nasarar lashe gasar bayan rashin nasara a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Turai.
Wasannin guje-guje da tsalle-tsalle
Daga ranar 19 zuwa 27 ga watan Agusta, Budapest babban birnin kasar Hungary zai kasance cibiyar dukkan masu sha'awar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle. Kimanin 'yan kallo 37,000 za su iya zama a cibiyar wasannin motsa jiki da aka gina musamman domin gasar cin kofin duniya. 'Yan wasan za su nuna bajinta a gudu da tsalle don samun lambobin yabo a jimillar fannoni 49.
Kofin duniya na kwallon Kwando
Za a gudanar da gasar kwallon kwando ta duniya daga ranar 25 ga Agusta zuwa 10 ga Satumba a Philippines da Japan da Indonesia. Har ila yau, tawagar Jamus a can tana fata - tare da daukan taurarin NBA a kusa da Dennis Schröder (hoto). Yin aiki mai kyau kuma zai zama abu mai mahimmanci saboda manyan kungiyoyi bakwai sun cancanci kaiwa zuwa gasar Olympics ta 2024 a Paris.
Kofin duniya na Cricket
Gasar cin kofin duniya ta Cricket za ta gudana ne a cikin kaka a kasar da ba wasu wasanni banda wasan Cricket. Indiya ce ke karbar bakoncin gasar karo na 13 a karo na hudu. "Maza sanye da rigunan kalar bula" suna da sha'awar lashe gasar duniya ta uku bayan 1983 da 2011. Ingila ce ke rike da kofin. Tun da farko, an shirya gudanar da gasar a watan Fabrairu, amma aka dage shi saboda COVID-19.
Wasannin sojoji nakasassun
An fara gudanar da taron wasanni na nakasassun sojoji tun daga shekarar 2014. Amma karo na shida zai gudana ne daga ranar 9 zuwa 16 ga Satumba a Düsseldorf. Kungiyoyin za su fafata don samun lambobin a wasannin guje-guje da tsalle-tsalle da wasan harbi da wasan kwale-kwale na cikin gida, da daga nauyi da tseren keken da wasan kwallon kafa da wasan ninkaya da zari ruga na guragu.
Gasar kwallon kafa ta Asiya
Tun da farko ya kamata a gudanar da gasar a kasar Chaina a watan Yuni da Yuli, amma Chaina ta fasa karbar gasar saboda annobar corona. Sabbin masu masaukin baki dai sun hada da Qatar mai rike da kofin gasar, wanda cikin mamaki ta doke Japan a wasan karshe na 2019. A saboda tsananin zafin hamada a rani, gasar cin kofin Asiya ta 2023 tabbas ba za ta gudana ba har sai Janairun 2024.