Manufofin Amirka kan nahiyar Afirka | Siyasa | DW | 24.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Manufofin Amirka kan nahiyar Afirka

Masana na ci-gaba da yin sharhi kan mahimmancin ziyarar shugaban kasar Amirka Barack Obama a kasashen Kenya da Habasha.

Sai dai kuma a daya hannun, wasu kuwa na masu cewa hakan ya nuna yadda Amirka da kasashen yamma suka damu da nausawar da kasar China ke yi a nahiyar Afirka.

Batun karfin da China ta yi a nahiyar Afirka dai tabbas abu ne kasashen yamma basa jin dadinsa, kuma dole idan Obama ya isa Habasha zai ga hakan. Domin ko da dakin taron da zai shiga da shugabannin Afirka shi ma kansa kasar China ce ta ginashi, kai hatta titin da Obama zai bi kafin ya isa gun taron kasar China ce ta shimfida shi, don haka batun China da Afirka za a iya cewa ya zamawa kasashen yamma ciwon ido. Wasu masanan irinsu Richard Downie, masanin siyasar kasar Amirka, sun bayyana wa DW cewa ziyarar Obama a Kenya na da dalilai masu yawa.

"Kenya dai kasa ce mai bin tsarin demokradiya, kuma tana fama matsalolin tsaro. Ko da fararen hular kasar sakamakon matsalolin tsaron suna cikin wani yanayin takurawa"

Dangantakar kasar Kenya da kasashen yamma dai ta yi rauni tun lokacin da shugaba Uhuru Kenyatta ya tsaya takara a zaben kasar shekaru biyu da suka gabata. Abinda masanan ke ganin a ziyarar ta Obama za ta nemi dinke barakar da aka samu.

"Huldar kasashen biyu tana da mahammmancin gaske. Kenya babbar kawace. Kamfanonin Amirka da yawa suna sarrafa kayansu a kasar Kenya ne. A bangaren tsaro ma kasar Kenya babbar kusa ce a yankin gabashin Afirka, kuma kasar na taka rawa wajen warware tashe-tashen hankulan yankin"

Baya ga kasar ta Kenya mai fama da rikicin kungiyar Al-Ashabab dake fitowa daga Somalaiya, Barack Obama zai kuma yiwa wani taron wakilan tsaron Kungiyar Tarayyar Afirka jawabi a birnin Habasha. Masini Richard Downie ya ce:

"Demokradiya da tsarin gudanar dashi dole a karfafa shi. Wasu kasashen Afirka da yawa tsarin demokradiyarsu na samun koma baya. Haka lamarin yake a kasar Habasha, dama ita kanta kasar Kenya"

Kenia USA Fotoreportage von Kogelo Dorf von Obamas Vorfahren

Kauyen Kogelo, mahaifar kanannin Barack Obama

Ko da yake akan ji shugabannin kasashen yamma na masu ambaton Afirka cikin tsarinsu ammafa a zahiri nahiyar Afirka ba ta da wani matsayin na azo a gani lamarin da masana suka tabbatar.

"Koda ma Afirka na da mahimmanci a tsare-tsaren Amirka, amma har yanzu tasirin Afirka bai taka kara ba, idan aka kwatanta da sauran nahiyoyi. Ofishin da ke luara da Afirka a ma'aikatar harkokin wajen Amirka kusan ba kudi a cikinsa, kuma kudaden kalilan ake bashi".

Idan dai ana batun demokradiyya to Obama da ba zai ziyarci kasar Habasha ba, domin mulkin mutun guda ake yi, masu adawa da gwamnati ba su da sakat. Don haka abinda zai kai Obaba shi ne kawai bukatun Amirka na fannin tattalin arziki siyasa da tsaro.

Sauti da bidiyo akan labarin