Manoman Tanzaniya za su samu tallafi | Himma dai Matasa | DW | 28.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Manoman Tanzaniya za su samu tallafi

Gwamnatin Tanzaniya na son inganta rayuwar masu kananan sana’oi. Manufar gwamnatin shi ne samar da karin abinci domin magance karancin abincin da za a iya fuskanta nan gaba.

Kokarin bunkasa harkokin noma a Tanzaniya

Kokarin bunkasa harkokin noma a Tanzaniya

Gwamnatin ta Tanzaniya dai na yin iyakacin bakin kokarinta wajen inganta walwalar kananan manoman kasar ta yadda hakan zai kai ga samar da abinci mai tarin yawa gami da tabbatar da ganin an samar da iri don amfanin gaba, a yayin da manyan kamfanoni ke tallafawa manoman duk kuwa da sukan da shirin yake samu daga bangarori daban-daban na kasar. Betrida Kayega tare na daga cikin manoman da suka ci gajiyar wannan shirin. Betrida mai shekaru 30 a duniya na cike da farin ciki akan irin amfanin da data samu a gonar shinkafarta ta kuma yi karin haske kan alfanun da ta samu tana mai cewa:

Samun amfanin gona mai yawa

"Mun samu amfanin gona fiye da da, a baya ina samun buhu takwas a eka guda amma yanzu haka ina samun buhu 30 a eka guda".

Kimanin manoma dubu 7,500 da suka futo daga yankin Kilombero ne ke taruwa guri guda domin kara bunkasa noman shinkafarsu, kuma suna karbar horo ne daga wani malamin gona mai suna Richard Hanga. Yana koya musu yadda za su rinka yin shuka kamar haka:

"Za ka rinka amfani da fatanya karama sai ka haka kananan ramuka a wajen da ka yi alama ta hanyar amfani da igiya santimita 25. In ka haka ramin sai ka zuba iri, sai dai kafin ka zuba irin zaka zuba taki sai ka sa irin sannan ka rufe ramin da kasa."

Gwamnatin Tanzaniya dai na son ta bunkasa wannan tsarin zuwa sauran sassan kasar. Sai dai kuma Kwarraru irin su Victor Manyong na cibiyar bunkasa ayyukan gona na nuna shakku akan lamarin, ya kuma ce:

Rashin tabbas kan matakin gwamnati

"Shin wannan wani tsari ne da za a kwafa kawai? Zan ce ba zai yiwu ba. Wannan wani tsari ne da za a kwafa sannan a fadada shi? Zan iya cewa eh, in zai yi wu. Sai dai ya kamata mu lura da kuskuren da aka tafka a Kilombero domin kada mu maimaita shi a wani wajen."

Manoman dai na fuskantar barazanar kwari da cuttuttuka da kuma ambaliyar ruwa. Sai dai kuma a lokaci guda wasu manoman na jin dadin yadda suke sayar da amfanin gonarsu ga KPL maimakon sayarwa dillalai, ko da yake malamin gona kuma manomi Richard na da ra'ayin cewa:

"Idan wani kamfanin kasar waje zai dinga kula da wannan shirin, dole ne su sa ka'idojinsu. Ka ga kananan manoma ba za su iya amfana sosai ba, to anan ne ya kamata gwamnati ta shigo tun daga farkon shirin domin gwamnati tana da karfi wajen shigar da manufofin ta."

Betrida Kayega da iyalanta dai na cin gajiyar amfanin gonar da suka shuka kana ta na kai wa kasuwanni ta sayar maimakon sayar da shinkafar ga kamfanin KPL.

Sauti da bidiyo akan labarin