Mane ya sa hannu kan kwantiragi da Bayern | Labarai | DW | 22.06.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mane ya sa hannu kan kwantiragi da Bayern

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta da ke jan zarenta a Bundesliga, tare da lashe gasar cin kofin zakarun Turai karo na 10 a jerea, ta gama yarjejeniyar siyan dan wasan gaba na Senegal Sadio Mane daga Liverpool.

Dan wasan gaba na aksar Senegal Sadio Mane ya sa hannu kan kwantiragin shekaru na taka leda a Bayern kan kudi kusan Yuro miliyan 40, sai dai Mane na da sauran shekara daya na murza leda a Liverpool.

Dan wasan mai shekaru 30 ya bar Anfield bayan buga wasanni 269, inda ya zura kwallaye 120 a dukkan wasannin da ya buga, wanda hakan ya taimaka wa kungiyar ta lashe gasar zakarun Turai a kakar wasa ta 2018-19 da kuma gasar Premier bayan kaka daya.

Dan wasan ya zama dan wasa na uku da Bayern ta dauko a karshen kakar wasa ta bana, bayan zuwan 'yan wasan Ajax Amsterdam Ryan Gravenberch da Noussair Mazrouai.