Manchester City ta lashe gasar lig-lig ta Ingila | Zamantakewa | DW | 13.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Manchester City ta lashe gasar lig-lig ta Ingila

Karo na biyu a jere, kungiyar Manchester City ta yi nasarar lashe gasar Premier Lieague ta Ingila karkashin mai horas da 'yan wasa Peo Guardiola.

A Ingila kungiyar Manchester City ta ciri tutar gwani bayan da ta gasa wa Brighton aya a hannu da ci hudu da nema, lamarin da ya bata damar zama zakara so biyu a jere bisa horaswar Pep Guardiola, kuma a karo na shida cikin tarihinta. Kungiyar Liverpool ce ta kasance a matsayi na biyu a bana sakamkon ratar maki daya da ke tsakaninta da City, alhali an samu lokaci da Liverpool ta tsere mata da maki bakwai, lamarin da ya susa wa mai horas da Liverpool Jürgen Klopp rai kasancewar rabon kungiyarsa ta lashe kambun zakara tun 1990 shekaru 29 ke nan da suka gabata.

Sai dai wasu 'yan wasan Premier League da ke da tushe da Afirka na da rawa a bana, kasancewa sune suka fi zura kwallo a raga. Hasali ma dai suna tafiya kafada da kafada ne domin kowannen su ya zura kwallaye 22 ne kama daga Pierre-Emerick Aubameyang dan asalin Gabon har i zuwa Mohamed Salah na Masar da Sadio Mane na Senegal.

A nan Jamus kuwa, Bayern Munich ta baras da damarta ta zama zakaran Bundesliga tun kafin ranar karshe, sakamakon ci nema da nema da ta yi da RB Leipzig da ke a matsayi na uku. Ita dai Yaya babba na bukatar samun nasara a wasan domin yi wa Dortmund da ke biya mata baya kintinkau tare da zama zakara a karo na bakwai a jere.

Ita ma  Borussia Dortmund tana tsammanin wa rabbuka a ranar karshe, kasancewa ratar maki biyu ke tsakaninta da Bayern Munich, bayan da ta samu nasara a kan Fortuna Düsseldorf da uku da biyu.

'Yan mata na kasashen yammacin Afirka sun yi nisa a kokarin da suke yi na lashe gasar kwallon kafa na wannan yanki da kasar Cote d'Ivoire ke daukar bakunci. Wannan dai ba shi ne karo na biyu da hukumar kwallon kafa ta kasashen yammacin Afirka ke shirya wannan gasa ba. Amma tuni aka samu kasashen da suka haye matakin kusa da na karshe bayan tankade da rairaya tsakanin 'yan mata na kasashe dabam-dabam. A rukunin farko, tun a ranar Asabar ne 'yan matan Ghana suka samu tikitin isa matakin kusa da na karshe bayan da suka doke takwarorinsu na Togo da ci shida da nema. Su kuwa 'yan matan Côte d'Ivoire sun yi nasarar lallasa na Senegal da ci hudu da nema, lamarin da ya basu damar ganin badi. Yayin da a rukunina biyu 'yan matan Mali sun fatattaki na Burkina Faso daga gasar bayan da suka dokesu da ci uku da daya. Su kuwa 'yan matan Najeriya wato Super Falconet sun yi wa 'yan uwansu na Nijar dukan fin karfi inda aka tashi wasan 'yan matan Najeriya na da ci 15 yayin da 'yan Nijar ke da nema.

Tennis 2019 Australian Open - Day 12 Novak Djokovic (Getty Images/M. Dodge)

Novak Djokovic dan Sabiya ke zama gwanin gwananaye na wasan Tennis a duniya

A fagen Tennis a ranar Lahadi aka gudanar da wasan karshe na Master din Madrid na kasar Spain, kuma Novak Djokovic ne ya lashe gasar sakamakon doke Stefanos Tsitsipas na Girka da ci 6-3, 6-4. Djokovic wanda da ma shi ne gwani na gwanayen Tennis a duniya, ya lashe kofi a manyan wasannin Masters guda 33, lamarin da ya bashi damar kafar ficeccen dan wasan Tennis nan wato Rafael Nadal.

A bangaren mata kuwa Kiki Bertens 'yar kasar Holland da ke da matsayi na bakwai a duniya ta lashe gasar bayan ta doke Simona Halep 'yar Romaniya da ke a matsayi na uku a duniya da ci 6-4, 6-4.

Sauti da bidiyo akan labarin