1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Malisar dinkin duniya Amurka sun koka da rashin aika dakarun kiyaye zaman lafiya na kungiyar AU zuwa Darfur---

Jamilu SaniOctober 6, 2004

Amurka ta ce zata baiwa kungiyar AU taimakon kudade---

https://p.dw.com/p/Bvfu
Hoto: AP

Majalisar dikin duniya da Amurka sun nuna matukar damuwar su game da batun jinkirta aika dakarun kiyaye zaman lafiya na gamaiyar Africa su 4,000 zuwa yankin Darfur dake fama da rikicin yan tawaye har sai nan da farkon shekara mai zuwa,don haka ne ma majalisar ta dikin duniya da Amurka suka bukaci kungiyar gamaiyar Africa data gagauta aika dakarun kiyaye zaman lafiya na kungiyar zuwa yakin Darfur ko hakan ya taimaka wajen kawo karshen fadan yan tawaye a wanan yanki.

Tun watan Afrilun da ya gabata kwamitin sulhu na majalisar dikin duniya ya sha faman tattauna yadda za’a kawo karshen hali na kaka na ka yi da alumar yankin Darfur ke fuskanta,inda daga karshe kwamitin sulhun na majalisar dikin duniya ya gabatar da wasu sabin kudirori guda biyu da suka bukaci kungiyar gamaiyar Africa ta kara yawan dakarunta data aika su 380 zuwa yanki na Darfur a matsayin masu shiga tsakani,wanda kuma har kawo yanzu kungiyar ta gamaiyar Africa bata sami sukunin aika karin dakarun nata zuwa yankin na Darfur ba mai fama da rikicin yan tawaye.

A yanzu haka dai manzon musanman na majalisar dikin duniya a Sudan Jan Pronk na cigaba da yin kira ga gwamnatin Sudan da kuma kungiyar gamaiyar Africa mai yawan kasahe 53,da su gagauta daukar matakan da suka dace na aika dakarun kiyaye zaman lafiya zuwa yankin Darfur,duk kuwa da cewar wasu dalilai zasu sanya a sami jinkiri na aika dakarun kiyaye zaman lafiya na gamaiyar Africa zuwa yankin na Darfur a matsayin masu shiga tsakani.

Jami’in na majalisar dikin duniya ya baiyana cewar tun da shike za’a sami jinkiri wajen aika dakarun kiyaye zaman lafiya na kungiyar AU,to kuwa kasahen duniya zasu aika dakarun su na kiyaye zaman lafiya zuwa yankin na Darfur har ya zuwa lokacin da kungiyar gamaiyar Africa zata aika dakarun nata zuwa yankin na Darfur farkon shekara mai kamawa.

Pronk ya kara da cewar tun da shike har yanzu yan tawaye sun gaza tsagaita wuta,kuma suna cigaba da kai hari kann fararen hular yankin na Darfur,to kuwa kamata yayi a ce an sami karin dakarun kiyaye zaman lafiya na kungiyar gamaiyar Africa zuwa yankin na Darfur cikin wanan watan.

Shi kuwa jakadan Amurka a Sudan John Danforth kira yayi ga kungiyar gamaiyar Africa ta gagauta aika dakarunta na kiyaye zaman lafiya zuwa yankin Darfru ba tare da bata wani lokaci ba.

A makon da ya gabata ne dai shugaba Olusegun Obasanjo na Nigeria,dake zaman shugaban kungiyar gamaiyar Africa,yace zasu gagauta aika dakarun kiyaye zaman lafiya na kungiyar AU 5,000 zuwa yankin Darfur,to amman kuma suna bukatar taimakon miliyoyin daloli daga kasahen duniya don aiwatar da wanan manufa.

Jakadan Amurka a Sudan Danforth ya baiyana cewar yana fatan yan majalisar datijan Amurka zasu amince a baiwa kungiyar gamaiyar Africa taimakon dola miliyan 75 cikin wanan shekarar don ta sami sukunin tafiyar da aiyukanta yadda ya kamata.