Mali ta kama wasu ′yan ta′adda kimanin 20 | Labarai | DW | 15.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mali ta kama wasu 'yan ta'adda kimanin 20

Daga cikin 'yan ta'addar har da wasu Faransawa biyu da kuma wani mutun da ake zargi da kitsa harin da aka kai a watan Maris a wani gidan cin abinci na birnin Bamako.

Hukumomin 'yan sandar kasar Mali sun bada sanarwar kama wasu mutane kimanin 20 da su ke zargi da kasance wa 'yan jihadi, ciki har da wasu Faransawa biyu da kuma wani mai suna Saouty Kouma da dama suke neman ruwa a jallo a bisa zarginsa da kitsa wani harin ta'addanci da aka kai ranar bakwai ga watan Maris a wani gidan cin abinci na birnin Bamako, da ya yi sanadiyyar mutuwar wani dan kasar Faransa guda da kuma wani dan kasar Beljiyam.

Hukumomin tsaron kasar Malin sun ce sun damke mutuman ne a ranar lahadin da ta gabata a garin Melo da ke a tsakiyar kasar ta Mali a yayin da sauran mutanan wadanda akasarinsu 'yan asalin kasar Moritaniya ne sun kama su ne a ran Litanin a garin Zegoua da ke a kudancin kasar ta Mali. Kuma tuni suka iza keyarsu zuwa birnin Bamako domin yi musu tambayoyi.