Mali ta daina sayar da hatsi ga ketare | Labarai | DW | 07.12.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mali ta daina sayar da hatsi ga ketare

Gwamnatin Mali ta fara rigakafin karancin abinci da kasar ke barazanar fuskanta sakamakon matsalar tsaro da fari. Fadar mulki ta Bamako, ta dakatar da fitar da shinkafa da masara daga cikin kasar zuwa kasashe makwabta.

A lokacin da yake bayani a wannan Talata, ministan bunkasa kasuwanci da masana'antun kasar Mali Mohamed Ould Mahmoud ya sanar cewa wannan mataki ne na kare kasar daga fadawa cikin ja'ibar 'yunwa. Ministan ya ce daminar bana ba ta yi kyau ba a Mali, a saboda haka ya zama wajibi su takaita fitar da dan amfanin gonar da suka noma domin ya wadaci kasar. 

Matakin da a cewar hukumomin Mali ya fara aiki daga jiya Litinin ya dakatar da kasar fitar da gero da dawo da sauran wasu kayan hatsi daga kasar.