Mali ta ceto mutanen da aka yi garkuwa da su | Labarai | DW | 21.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mali ta ceto mutanen da aka yi garkuwa da su

Gwamnatin Mali ta kafa dokar ta baci a fadin kasar tare da kawo karshen garkuwa da mutane a otel da aka kai hari a Bamako babban birnin kasar.

Shugaba Boubakar Keita na Mali ya kafa dokar ta baci na kwanki goma a kasar tare da ayyana zaman makoki na kwanaki uku, bayan da wasu 'yan bindiga suka kai hari a wani hotal na Bamako, inda suka kashe mutane kimanin 27, tare da yin garkuwa da wasu 170. Sai dai kuma sojojin kundumbala na Mali tare da taimakon takwarorinsu na kasashe makwabta sun yi nasarar kutsawa cikin hotal din mai suna Radisson Blu, inda suka ceto wadanda aka yi garkuwa da su. Kungiyar Al-Murabitun da ke da alaka da IS ce ta daukai alhakkin wannan harin.

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya nuna damuwa dangane da wannan hari na Bamako, inda ya ce ya zo ne a daidai lokacin da Mali ta fara samun ci gaba a kokarinta na dinke barakar da ke damunta. Shi kuwa shugaban Amirka Barack Obama ya ce wannan harin ya sa su kara daura damarar tinkarar ayyukan ta'addaci a cikin duniya.

Wani bangare na kasar Mali ya taba fadawa hannu masu tsaurin kishin addini shekaru ukun da suka gabata, kafin a yi nasar kwatoshi bisa taimakon sojojin kasar Faransa.