1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru uku na mulkin rikon kwarya a Mali

August 24, 2020

Sojojin da suka kifar da gwamnatin kasar Mali, sun bukaci ci gaba da rike ragamar kasar na tsawon shekaru uku, bayan ganawar da tawagar kungiyar ECOWAS mai shiga tsakani kan rikicin Mali.

https://p.dw.com/p/3hQeq
Mali Putsch Pressekonferenz
Hoto: picture-alliance/dpa

Sojojin Mali bayan batun mulkin tsawon shekarun uku da suka nuna bukata, sun kuma amince za su saki hambararren Shugaba Ibrahim Boubacar Keita da sauran shugabanni na siyasa da suke rike da su a halin yanzu. Manufar sojojin shi ne shirya gwamnatin hadaka da za ta tsara sabon zabe karkashin jagorancin shugaba na mulkin soja lamarin da ya fito fili da cewa manyan da za su ja ragamar kasar za su kasance sojoji ne galibin su.

An dai kifar da gwamnatin Malin ne a makon jiya, bayan zanga-zangar watannin da aka jima ana adawa da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita a yayin tattaunawar da aka fara a karshen mako, sojojin sun bayyana bukatunsu duk da cewar har yanzu ba a kai ga cimma matsaya ba tsakanin manzon na musamman na kungiyar ECOWAS da sojojin da suka hambarar da gwamnati a Mali.

Kakakin sojojin na Mali  kanal Ismael Wague, ya shaida wamanema labaru cewar, babu wani abin gaggawa saboda ana samun fahimtar juna yana mai cewa "za a ci gaba da tattaunawa kan da bangarorin da kungiyar ECOWAS ta ta aiko."

Shi mamanzo na musamman na kungiyar ECOWAS kuma tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathanya bayyana cewa da akwai alamun samun nasara, inda ya ce "Abin da muke muradin baki dayanmu a nan shi ne ci gaban Mali. Ina nufin da sojojin da mu wakilan ECOWAS manufarmu guda ce. Mun cimma wadansu daga cikin bukatun dukkanin bangarorin, sai dai har yanzu dai bamu kai ga tikewa ba." To sai dai Goodluck Jonathan ya ce babu abin gaggawa, lokacin da masu aiko da rahotanni suka matsa.

Kasashe masu makwabtaka da Mali na ci gaba da tsayawa kan bukatar maido da Shugaba Ibrahim Boubacar Keita kan kujerarsa, duk da cewar alamu na ci gaba da nuna wahalar hakan.

Za a dora kan tattaunawar a yau Litinin a Bamako, kamar yadda ta tabbata a iya Lahadi, bayan zama na kwanaki biyu da aka yi da sojojin da suka kifar da gwamnatin Malin.