1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: Samar da makamashi a makarantu

Madelaine Meier/Nura Datti/Gazali AbdouJanuary 6, 2016

Injiniya Makan Tandina ya fara anfani da fasahar hasken rana wajan wadata makarantun yankunan karkara da wutar don dalibai su sami damar yin karatu.

https://p.dw.com/p/1HZBu
AOM Filmstill - Mali Solar Energy
Hoto: DW

Kasar Mali da ke yankin yammacin Afrika na fama da karancin wutar lantarki, in da take samun taimakon makamashi daga kasar Cote d'Ivoire, sai dai daya daga cikin Injiniyoyin kasar Makan Tandina ya fara anfani da fasahar hasken rana wajan wadata makarantun yankunan karkara da wutar don dalibai su sami damar yin karatu.

A garin Farako na kasar Malin, yara ba sa son komawa gida bayan sun tashi daga makaranta, duk kuma da cewa dare ya fara yi, saboda a nan ne suke iya samun damar yin nazari ba tare da matsala ba. Wutar lantarki na samuwa ne a wannan makaranta a kafatanin wannan kauye, kamar yadda wata daliba ta fada.

 "Muna farin ciki da samun wutar lantarki, domin tana bamu damar yin nazari da maraice, Sannan bayan cin abincin dare, muna dawowa mu yi wasa".

Gudunmuwar Tandina a fannin samar da makamashi a makarantu

AOM Filmstill - Mali Solar Energy
Hoto: DW

Makan Tandina ne yake samar da wutar ta lantarki daga fassahar sarrafa hasken rana. Shi dai injiniyan ya yi karatunsa ne a Faransa inda yake da damar samun albashi mai tsoka, sai dai kuma ya dawo gida ne don bayar da gudunmawarsa a fannin samar da makamshi, saboda babban fatansa shi ne ya ga kasarsa ta Mali ta anfana da basirar da Allah ya huwace masa.

"Wannan wani abu ne da nake alfahari da shi, duk da cewa ba ni na samar da kudin aiwatar da shi ba, amma ina mai farin cikin cewa ni na aiwatar da wannan aikin tun daga farkonsa har karshe, don haka ina jin cewar rayuwata ta yi amfani a duniya".

Makan ya kasance yana yawan saka ido a kan tsarin samar da wutar lantarki don ganin komai yana tafiya cikin tsari. Wannan matashi mai shekaru 29 ya samu kwantiraginsa na farko daga mahukuntan kasar na kafa wata karamar tashar samar da hasken wutar lantarki a wasu kauyuka, duk da cewar akwai kalubale.

"A wancan karon da muka zo dasa inji, da kwale-kwale muka yi ta jigila, in da ya daukar mana lokaci mai tsayi, Sannan kuma aikin ya tara mana gajiya, amma kuma wani bangare ne na aikinmu, amma kuma muna shan wuya wajen shiga wasu baudaddun kauyuka".

AOM Filmstill - Mali Solar Energy
Hoto: DW

Harakokin Makan Tandina na samun bunkasa a kasar Mali

MakanTandina dan asalin Arewacin Mali ne wato birnin Timbuktu, ya kuma fahimci amfani da rana wajen samar da lantarki, ofishinsa na cike da takardun yarjejeniyoyin cinikayya da ya cimma don kaddamar da sabbin ayyuka. Sabo da hake ne yake yawan buga waya da rubuce-rubuce.

"Makamashi muhimmin ginshinkin ne na rayuwa daidai da ruwan sha. Saboda haka lantarki ma wani bangare ne na rayuwa".

Sai dai wani babban abin da yake dada faranta ran Makan Tandina shi ne yadda rayuwa ta inganta a Farko sakamakon lantarki, nazarin dare da dalibai ke yi ya fara samar da cigaba a wannan yanki, sakamakon yadda daliban suka taka rawar gani a galibin sakamakon jarrabawarsu da ta fita. ))