Mali na kokarin sake kwato yankin Kidal | Labarai | DW | 19.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mali na kokarin sake kwato yankin Kidal

Mali ta tura dakaru don sake kwato garin Kidal da ke arewacin kasar daga hannun 'yan tawaye wadanda suka farma ginin gwamnan yankin tare da kashe sojoji.

A wannan Litinin gwamnatin Mali mai karfi a Bamako babban birnin kasar, ta tura dakaru don kwato tungar 'yan tawaye da ke Kidal bayan 'yan awaren Abzinawa sun kwace gine-ginen kananan hukumomi kana sun yi garkuwa da mutane abin da ya janyo musayar wuta da sojoji da yi sanadiyyar asarar rayuka masu yawa. Wata majiyar rundunar sojojin Mali ta fada wa kamfanin dillancin labarun AFP cewa ta dauki duk wani mataki da ya dace na karfafa kasancewarta a arewacin kasar. Majiyar ta kara da cewa tun a ranar Asabar sojoji suka fara isa yankin sannan wasu na kan hanya daga garin Gao zuwa Kidal. Sojoji takwas da 'yan aware 28 suka rasu a fadan da aka yi a ranar Asabar a wajen ofishin gwamnan yankin sannan sojojin sa kai sun yi garkuwa da ma'aikata kusan 30.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe