Mali na fama da hare-haren ta′addanci | Labarai | DW | 09.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mali na fama da hare-haren ta'addanci

Kwana guda bayan mummunan hari a Mali wasu 'yan bindiga sun hallaka fararen hula 10 a wani sabon hari da suka kai a arewacin kasar.

Mali na fuskantar hare-hare

Mali na fuskantar hare-hare

Kakakin rundunar sojojin kasar Souleymane Maiga da ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce harin an kai shi ne a kauyen Gaberi da ke arewacin kasar ta Mali. Wannan harin dai na zuwa ne kwana guda bayan da wasu da ake kyautata zaton masu kaifin kishin addini ne suka kai hari a wani Otel ta re da yin garkuwa da mutanen da ke ciki inda suka hallaka mutane 12 ciki kuwa har da jami'an Majalisar Dinkin Duniya hudu kafin a samu nasarar kawo karshen garkuwar da suka yi da mutanen. Kawo yanzu dai babu wani ko wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.