Mali na cikin juyayi na asarar sojojin ta | Labarai | DW | 22.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mali na cikin juyayi na asarar sojojin ta

Majiyoyin soji a Mali, sun tabbatar da mutuwar sojoji guda uku a yanki tsakiya na kasar bayan da motar da ke dauke da su ta taka wasu abubuwa da suka yi bindiga.

Majiyar ta ce motar da ke dauke da sojojin ta taka wasu abubuwan da ke fashewa a kusa da Mondoro kan iyaka da Burkina Faso inda 'yan ta'adda ke dada kai hare-hare. Kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso na fuskantar tashin hankali na hare-hare 'yan ta'ada tun daga shekara ta 2015 wanda kawo yanzu sama da mutane dubu 15 suka mutu a cikin tashin hankalin  a cikin kasashen uku.