1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS ta kara takunkumai ga Mali

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 13, 2022

Tun bayan da sojoji suka yi juyin mulki har sau biyu cikin shekara guda a Mali, kasashen duniya da ma kungiyoyi ke ta yin tir da matakin na soja. Kungiyar ECOWAS ko CEDEAO da takwararta ta AU sun sakawa Malin Takunkumi.

https://p.dw.com/p/45VEy
Mali | shugaban gwamnatin rikon kwarya Assimi Goïta
Shugaban gwamnatin mulkin soja ta Mali Assimi GoïtaHoto: Präsidentschaft der Republik Mali

Jagoran mulkin soja na kasar Malin Assimi Goïta dai, ya bayyana matakin kakabawa kasarsa sababbin takunkumai da kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAs ko CEDEAO ta a matsayin mai tsauri da kuma rashin amfani. Gwamnatin mulkin sojan ta Mali ta bukaci magoya bayanta a kasar da su fito su nuna adawarsu da matakin na ECOWAS ko CEDEAO, inda tun a ranar Litinin din wannan makon, al'ummar kasar da ke goyon bayan mulkin sojan suka fara gudanar da wani gangami domin yin tir ga sababbin takunkuman na ECOWAS ko CEDEAO.

Ra'ayoyi dai sun bambanta tsakanin al'ummar Malin, inda was ke nuna halin ko in kula da matakin na kungiyar ECOWAS ko CEDEAO kana wasu kuma ke nuni da cewa za su jure wahaalar da za su shiga. Matakin na kungiyar  Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma dai, ya hadar da rufe kan iyakokin sama da na kasa a Malin da janye tallafin kudi da kasuwanci tsakanin kasashe yammacin Afirka da kuma janye dukkan jakadun kasashen ECOWAS daga kasar. 

Tuni dai al'ummomin kasashen da ke makwabtaka da Malin suka fara mayar da martani, inda a Jamhuriyar Nijar al'umma ke tafka muhawara kan dacewa ko rashin dacewar matakin na ECOWAS ko CEDEAO. Kawancen kungiyoyin farar hula na Tournons la Page a Nijar din na daga cikin masu adawa da matakin, inda cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta yi tir da shi.