1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IBK ya sake lashe zaben shugaban kasa a Mali

Yusuf Bala Nayaya GAT
August 16, 2018

Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya samu sama da kashi 60 cikin dari a zaben shugaban kasa zagaye na biyu da aka yi ranar Lahadi kamar yadda hukumar zaben kasar ta bayyana sakamako.

https://p.dw.com/p/33Gjf
Nigeria Ibrahim Boubacar Keita in Abuja
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Sakamakon zaben shugaban kasar ta Mali zagaye na biyu da hukumar zaben kasar ta bayyana a ranar Alhamis, ya nunar da cewa shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita ya doke jagoran 'yan adawa Soumaila Cisse bayan da ya samu kaso mafi yawa a kuri'un da aka kada a zaben, kamar dai yadda ministan kananan hukumomi Mohamed Ag Erlaf ya sanar a kafar talabijin ta kasar. A cewar Mohamed Ag Erlaf mutane miliyan takwas da dari hudu da sittin da biyu ne suka yi rijistar zaben kuma Shugaba Keita ya samu sama da miliyan daya na kuri'un kamar yadda yake karin haske:

"A sakamakon zaben, Mista Ibrahim Boubacar Keita ya samu kuri'a 1,798,632 wato kashi 67.17 cikin dari, yayin da jagoran adawa Mista Soumaila Cisse ya samu kuri'u 879,235; wato kashi 32.83 cikin dari."

Mutane dai ba su fita zaben ba kamar yadda ya kamata, an samu kashi 34.5 ne kawai cikin dari saboda fargabar tsaro kamar yadda shi ma Mohamed Ag Erlaf ya bayyana cikin jawabinsa ga manema labarai.

Präsidentschaftswahlen Mali

Sai dai jagoran adawa Soumaila Cisse ya yi watsi da sakamakon zaben tun ma kafin a bayyana bisa zargin cewa an tafka magudi. Amma a nasu bangaren masu sanya idanu a zaben kamar wakilan Kungiyar Tarayyar Turai sun bayyana cewa sun gano wasu kura-kurai a lokacin zaben amma ba tafka magudi ba kamar yadda jagorar masu sanya idanun daga kungiyar ta EU Cecile Kyenge ke cewa:

"Zan iya tabbatar da cewa masu sanya idanunmu ba su ga tafka magudi a zaben ba, amma dai sun ga kura-kurai kan yadda aka bi tsarin zaben daki-daki misali an ki bayyana sakamako bainar jam'a a cibiyoyin kada kuri'a sama da kashi daya bisa uku na cibiyoyin kada kuri'a da wakilanmu suka ziyarta. Kashi 14 cikin dari na wasu wuraren zaben a sirrance suke."

'Yan adawar da suka yi fatali da wannan sakamakon zaben shugaban kasa na wannan rana ta Alhamis sun kuma ce za su yi duk abin da ya wajaba na ganin sun kalubalanci sakamakon kamar yadda dimukuradiyya ta tanada, kasancewar sakamakon da suka gani ya saba da abin da ke zama na zahiri kamar yadda Tiebile Drame da ke zama jagoran yakin neman zabe na Soumaila Cisse jagoran adawa ya bayyana. To ko su al'umma me suke cewa game da zaben na Mali? Al- Ousseini wani dan jarida ne mazaunin birnin Tombouctou.

Mali Präsidentschaftswahl 30./31. Juli Soumaila Cisse
Hoto: DW/K.Gänsler


"A nan birnin Tombouctou lamurra na tafiya kamar yadda aka saba, jama‘a na gudanar da harkokinsu na yau da kullum. Ko da shi ke cewa a wuraren taruwar jama’a za ka tarar mutane na ta tsokaci kan sakamakon zaben, to amma babu abin da ya sauya a yanayin rayuwa, kai ka ce ba a lokacin zabe muke ba. A takaice za a iya cewa a wajen al’ummar Tombouctou ranar zabe ce kawai ta ke da muhimmanci, bayan kammala zaben kowa ya shiga harkokinshi."


Kasar ta Mali wacce ke a yankin yammacin Afirka dai ta ci gaba da fuskantar kalubale ta fuskar matsalar tsaro tun bayan da Keita ya kada Cisse a zagaye na biyu na irin wannan zabe da aka yi a shekarar 2013. Masu kai hare-hare da sunan addinin Islama sun baza ayyukansu a tsakiyar Mali inda mayakan Al-Ka'ida da IS ke dabdalarsu baya ga rigingimu na kabilanci, lamarin da kan harzuka zukata da ma sanya rashin yarda da mahukunta.