Mali: Harin kwanton bauna ya hallaka sojoji uku | Labarai | DW | 01.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mali: Harin kwanton bauna ya hallaka sojoji uku

Rundunar sojojin Mali ta sanar da mutuwar sojojinta guda uku, sannan kuma wasu sojojin kasar Faransa guda takwas sun samu raunuka sakamakon wani harin ta'addanci.

MINUSMA Soldaten UN Mission Mali (AFP/Getty Images)

Dakarun MINUSMA a kasar Mali

Tun da wajejen karfe takwas da minti 40 ne na safe agogon kasar ta Mali, lamarin ya afku a sansanin dakarun Majalisar Dinkin Duniya na MINISMA da ke birnin Tombouctou a cewar mai magana da yawun dakarun sojojin kasar Faransa Kanal Patrik Steiger, wanda ya ce daya daga cikin sojoji takwas na Faransa da suka ji ciwo na cikin mawuyacin hali. Daga nata bangare rundunar sojojin kasar ta Mali cikin wata sanarwa, ta ce maharan sun halba wani babban makami ne a filin tashi da saukar jiragen sama na Tombouctou.