Mali: Fulani makiyaya fiye da 100 sun mutu | Labarai | DW | 23.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mali: Fulani makiyaya fiye da 100 sun mutu

Wasu jerin hare-hare da 'yan bindiga suka kai a wannan Asabar sun yi sanadiyar mutuwar Fulani makiyaya akalla 110, ana fargabar alkaluman mamatan ka iya karuwa.

Moulaye Guindo, wanda shi ne Magajin garin Bankass daya daga cikin kauyukan yankin da aka kai harin, ya ce maharan sun shigo kauyen ne, sanye da tufafi irin na mafarauta, abin da ya sa suka iya kai harin kafin ma jama'a su farga. Rahotannin da ke fitowa daga kasar,  sun danganta harin da wata kwantanciyar rikicin kabilanci da al'ummar yankin suka dade suna fama da su.