Mali: An kashe wasu masu jihadi | Labarai | DW | 03.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mali: An kashe wasu masu jihadi

Dakarun kasar Faransa, sun yi arangama da masu tayar da kayar baya a arewacin kasar Mali, inda rahotanni suka ce akalla mayakan tawayen akalla 20 suka mutu.

Dakarun da ke cikin rundunar Barkhan ta hadin guiwar kasashe masu yaki da ta'addanci a Mali da sauran kasashen yankin Sahel, sun kai wa mayakan tawayen farmaki ne ta sama ta hanyar amfani da jiragen helkofta da kuma wasu samfurin Jet Jet na yaki.Bayanai sun kuma ce akwai wasu sojojin rundunar hudu da suka jikkata, sakamakon harba rokokin da 'yan tawayen suka yi kan daya daga cikin sansanonin sojojin da ke a Timbuktu. Haka nan ma kawana guda kafin wannan arangamar, 'yan tawayen sun hallaka wani sojan Mali daya a wata kwantan bauna.