Faransa ta hallaka kusa a kungiyar al-Qa'ida
November 13, 2020Talla
Mutumin mai suna Bah Ag Moussa ya gamu da ajalinsa ne a yayin wani farmakin da rundunar tsaron Faransa mai yaki da ta'addanci Barkhane ta kai kan tawagarsa a yankin Menaka da ke Arewa maso gabashin kasar Mali, kana kuma harin ya hallaka wasu mutane hudu da ke yi masa rakiya.
Kakakin ma'aikatar tsaron Faransa ya ce Bah Ag Moussa na daya daga cikin jerin mamanyan hafsansoshin mayakan jihadin, kana kuma yana daya daga cikin masu daukar wa kungiyar GSIM mai alaka da Al-Qaïda mayaka, sannan kuma yana da hannu wajen kitsa kai muggan hare-haren ta 'addanci kan sojojin Mali da da kawayenta.