1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Malawi: Zabiya na zama cikin kuncin rayuwa

February 12, 2019

Kasar Malawi na daya daga cikin kasashen Afirka inda zabiya ke rayuwa cikin fargaba sakamakon camfa su da wasu al'umar kasar suka yi, kungiyar kare hakkin zabiyar ta bukaci gwamnati ta kara kaimi wajen kare su.

https://p.dw.com/p/3DCkP
Mosambik Albinos in Quelimane
Hoto: DW/M. Mueia

Kandanji Banda zabiya ne mai shekaru 28 a birnin Salinma dake yankin Lakeshore a kasar Malawi. Matashin sanye da hula da tabarau da kuma riga mai dogon hannu yana kaucewa duk wanda ya rabe shi saboda yadda ake farautar su. Ya baiyana irin rayuwar cikin tsoron da suke yi a kasar.

Yace rayuwar na cikin hatsari, muna gudanar da rayuwa cikin rashin tabbas domin bamu san me zamu fuskanta ba a kullum, Allah na ke godewa kullum idan na ga na farka daga barci, ban san lokacin da zan gamu da tsautasyi ba, ba sai cikin dare ake farautar mu ba da rana ma kame mu ake yi.

Shekaru biyu da suka gabata, a Malawi kai wa zabiya hari ya zama ruwan dare, al'amarin da yake neman ya gagari gwamnati, Kandanji ya ja hankalin mahukantan kasar da cewa

Rene und Clifford Bouma aus Kamerun
Wasu Zabiya Rene da kuma Clifford BoumaHoto: Rene und Clifford Bouma

“Muna rokon gwamnati da ta kare mu, mun yi yunkuri da dama amma ba wani sakamakon da ya biyo baya, kasancewar har yanzu a wannan kasa ana satar zabiya a kashe, abin takaici ne, yadda ake zargin kungiyarmu da sukar gwamnati, maimakon a dauki matakin tsaro, muna mamakin yadda shari'ar wadanda aka samu da laifin kamewa da kisan zabiya ta tsaya."

Kasar ta Malawi kamar wasu kasashen Afrika sun camfa zabiya, lamarin da ya jefa su cikin masifa, Overstone Kondowe shine shugaban kungiyar ta zabiya ya dora alhakin wannan matsala kan gwamnati.

“Yace za mu yi wani gangami a fadar gwamnati, har sai hukuma ta dauki matakin gaggawa, mun gabatar da bukatu biyar da suka hada da bukatar shugaban kasa ya yi aiki akai.

Yanzu haka dai Shugaban Malawi Peter Mutharika ya yi Allah wadai da kakkausar murya da masu kashe zabiya a fadin kasar bayan ya umarci ‘yan sanda su basu kariya