1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Malawi na fama da mummunar fari

Abdourahamane HassaneApril 13, 2016

A cikin wata sanarwa da ya bayyana shugaban Ƙasar Malawi Peter Mutharika ya ce farin da yankin Kusurwar Afirka yake fama da shi fiye da shekara guda ya janyo ƙaranci abinci

https://p.dw.com/p/1IUiD
Flüchtlingslager in Kapise, Malawi
Hoto: HRW

A cikin wata sanarwa da ya bayyana Mutharika ya ce farin da yankin Kusurwar Afirkan yake fama da shi fiye da shekara guda ya janyo ƙaranci abinci wanda ya ce za a yi samun faduwar amfanin gonar da ake samu da kishi 12 cikin dari.

Abin da ya ce zai sa a samu ƙarin jama'ar da za su buƙaci agajin gaggawa. Hukumar abinci ta MDD PAM ta ce ta kai ɗauki ga mutane miliyan uku a yakuna 23 cikin 28 da ke fama da yunwa.Farin wanda ya afkawa yankin Gabashi da kuma na Kudacin na Afirka wanda ya janyo mumunar yunwa,ya shafi ƙasashen Zimbabuwe da Zambiya da Mozambik da kuma Afirka ta Kudu ta kudu tun shekarar bara