Makwabtan Libiya sun yi kira da a yi sulhu a ƙasar | Labarai | DW | 25.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Makwabtan Libiya sun yi kira da a yi sulhu a ƙasar

Ƙasashe da ke maƙwabtaka da Libiya sun ce ba za su yi katsalanda a harkokin cikin gidan ƙasar ba, amma sun yi kira da a sasanta.

A cikin sanarwar bayan taron da suka yi a birnin Alƙahira na ƙasar Masar a wannan Litinin, ƙasashe masu maƙwabtaka da Libiya sun amince cewar ba za su yi katsalanda cikin harkokin ƙasar don kawo ƙarshen ruɗani da tashe-tashen hankula a ƙasar mai arzikin man fetir ba. Maimakon haka ƙasashen kira suka yi da a nemo hanyar sassanta al'ummar ƙasar. Matakin na hadin guiwar ƙasashe maƙwabtan ya dace da manufarsu ta ƙin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Libiya. Da farko jakadan Libiya a birnin Alkahira ya buƙaci gamaiyar ƙasa da ƙasa ta taimaka a samar da kariya ga rijiyoyin mai da filayen jiragen sama da kuma sauran ƙadarorin ƙasa.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdourahamane Hassane