1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makuddan kudaden sallama ga jami'ai a Kenya

January 12, 2013

Shugaban Kenya yayi watsi da dokar baiwa 'yan majalisar dokoki kudaden sallama na dala 110,000.

https://p.dw.com/p/17J20
Opposition leader Raila Odinga, left, looks on as Kenyan President Mwai Kibaki, right, announce the cabinet and Odinga as the Prime Minister, Sunday, April 13, 2008 at State House in Nairobi, Kenya. President Mwai Kibaki on Sunday named rival Raila Odinga as prime minister, implementing a power-sharing deal after protracted negotiations over the deal they signed over a month ago.(AP Photo/Karel Prinsloo)
Hoto: AP

Shugaban Kenya ya hau kujerar na-ki game da dokar da 'yan majalisar dokokin kasar suka zartar, a lokacin zamansu na karshe, inda suka amince da baiwa kawunansu garabasar kudade gabannin gudanar da zabukan kasar. A wannan Asabar ce shugaba Mwai Kibaki ya baiwa babban mai shari'a na kasar umarnin sake tsara dokar, ta yadda za ta dace da tsarin mulkin kasar.

Kudirin dokar da 'yan majalisar suka yi naa'am da shi a ranar Larabar da ta gabata dai, ya tanadi baiwa kowane dan majalisar dokoki daya kudi dalar Amirka dubu 110, a matsayin kudin sallama. Hakanan a karkashin dokar, kowane dan majalisa zai sami jami'in tsaron lafiyarsa, da fasgo irin na diflomasiyya da kuma matsayi - irin na manyan jami'ai a tashoshin jiragen sama.

Sai dai kuma hukumar kula da harkokin albashi da alawus-alawus ta kasar Kenya ta ce matakin da 'yan majalisar dokokin suka dauka ya sabawa doka - a karkashin tsarin mulkin da kasar ta yi na'am da shi a shekara ta 2010. A dai kasar Kenya matsakaicin ma'akaikaci na karban albashin kimanin kudi dala 1,700 ne a duk shekara.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita        : Mouhamadou Awal Balarabe