Makomar ′yan tawayen M23 a Kongo | Labarai | DW | 11.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Makomar 'yan tawayen M23 a Kongo

Gwamnatin jamhuriyyar Dimokradiyyar Kongo ta gindaya sharadin afuwa ga 'yan tawayen gabashin kasar.

Gwamnatin jamhuriyyar Dimokradiyyar Kongo ta fadi - a wanman Litinin cewar, za ta yi afuwa ga 'yan tawayen gabashin kasar tare da sanya su cikin rundunar sojin kasar - muddin dai suka amince da ajiye makamansu a karshen wannan makon. Sai dai kuma wani jagoran 'yan tawayen ya ce akwai bukatar ci gaba da tattaunawa tukuna. Wannan tayin dai ya yi kama da na baya, wanda ke da nufin kawo karshen rigingimun da ke wanzuwa a yankin gabashin kasar, wanda ke da arzikin ma'adinai, inda kuma sha'anin siyasa da kabilanci da kuma zaman dar-dar tare da Ruwanda ke ci gaba da hana ruwa gudu a zaman lafiyar kasar na kusan kimanin shekaru 20. A dai shekarar da ta gabata ce kungiyar 'yan tawayen M23 ta kwace iko da garin Goma da ke zama hadikwatar yankin gabashin kasar ta Kongo na wani dan takaitaccen lokaci, lamarin da kuma ya kasance abin kunya ne ga dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da ke tallafawa sojojin kasar ta Kongo.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou