Makomar tsohon shugaban Masar | Labarai | DW | 12.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Makomar tsohon shugaban Masar

Jamus ta bukaci hanzarta sakin shugaban Masar Mursi, a matsayin wani bangare na warware rikicin kasar.

Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle yayi kira da a gaggauta sakin hambararren shugaban Masar Mohammed Mursi. A cikin jawabin da yayi a birnin Berlin, fadar gwamnatin Jamus, mai magana da yawon ministan, Martin Shaefer ya ce babu abin da duk wani tashin hankalin siyasar zai haifar akan kasar ta Masar in banda jefa ta a cikin mawuyaciyar makoma. A don haka yace, Jamus ta bukaci da a kawo karshen tsare Mohammed Mursi da ake yi . Ya kara da cewa, akwai bukatar ba wata kungiya ta kasa da kasa mai zaman kanta kamar ta Red Cross damar ganawa da Mursi ba da wani sharadi ba. Ba'ada bayan haka, ana jinkirta kafa gwamnatin wucin gadi.

To sai dai firaiministan rikon kwaryar Masar, Hassam al-Beblawai ya fada wa kamfanin dillancin labarun Reuters cewar, za a kafa gwamnati kafin karshen mako mai zuwa. Da farko Beblawi ya kyautata fatan kafa gwamnati a ranar Litinin mai zuwa.

A daura da hakan Kungiyar 'yan uwa Musulmi da ke nuna goyon baya ga Mursi ta ce za ta ci gaba da gudanar da zanga-zanga har sai an sake dora Mursi kan karagar mulkin kasar.

Mawallafiya : Halima Balaraba Abbas

Edita : Saleh Umar Saleh