Makomar tsaro a Afghanistan daga 2014 | Labarai | DW | 21.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Makomar tsaro a Afghanistan daga 2014

Majalisar mashawarta ta Afghanistan da aka sani da Loya Jirga ta na zama a Kabul domin nazarin yarjejeniyar tsaro da ake shirin cimma tsakanin kasar da Amirka.

Kasar Amirka da takwarta ta Afghanistan sun cimma matsaya game da yarjejeniyar tsaro da za su sa hannu a kai, wacce ta tanadi horas da sojojin Afghanistan bayan janyewar sojojin NATO daga kasar a shekara a badi. Wannan sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da majalisar mashawartan Afghanistan za ta fara zama, a wannan Alhamis a birnin Kabul, domin tattauna batun yarjejeniyar tsaro tsakaninta da Amirka.

Amirka za ta ci-gaba da zama a Afghanistan domin hana kasar sake fadawa cikin wani sabon tashin hankali bayan ficewar dakarun NATO, idan 'yan majalisan suka amince da wannan kudiri. Wannan yarjejniya dai za ta amince cewa ba za a gurfanar da sojojin Amirka a gaban kotun kasar Afghanistan ba, komin laifi ko ta'asar da ya tafka.

Da ma tun da farko fadar mulki ta White House, ta yi barazanar juya wa hukumomin Kabul baya, idan ba su amince da sharudan da suka gindaya kafin a cimma yarjejeniyar tsaro tsakaninsu ba.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Usman Shehu Usman