1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aikin sojin Jamus a Mali da corona a Afirka a jaridun Jamus

Zainab Mohammed Abubakar MAB
July 2, 2021

Jaridar Die Welt ta nuna cewar ana samun karuwar masu kamuwa da corona sakamakon sabon nau'in cutar na Delta. Yayin da jaridar der Freitag ta ce kamata ya yi Jamus ta janye soji daga Mali kamar yadda ta yi a Afganistan.

https://p.dw.com/p/3vwv9
Illustrationsfoto „Afropresse"
Hoto: DW/H. Flotat-Talon

Jaridar Die Welt ta ta rubuta sharhi mai taken "Shin Afrika na gazawa ne a yakin da take yi da annobar corona?", inda ta ce ana samun raguwar yawan masu kamuwa da Covid-19 a sassan duniya. Sai dai labarin daban yake a kasashe Afirka da ke yankin kudu da sahara. Hakan ba zai kasa nasaba da sabon nau'in cutar mai suna Delta ba. Ana iya ganin ta'azzarar sabon nau'in cutar ta corona zagaye na uku a kasar Namibiya. Lamarin sai kara ta'azzara yake a sauran kasashen Afirka inda tun a tsakiyar watan Yuni, aka ruwaito karuwar sabbin masu kamuwa zuwa kaso 40 daga cikin 100.

Masu shiga tsakani a bangaren Jamus sun yi fatan cimma warware takaddamar kisan kiyashin da ya auku lokacin mulkin mallaka ga 'yan kabilar Herero a wannan kasa da ke yankin kudancin Afirka. Duk da yarjejeniyar da aka cimma, an samu cikas ne saboda rashin jituwa tsakanin wakilan kabilar ta Herero a tattaunawar, sai dai uwa uba watakila saboda ta'azzarar corona. A watan Mayu shugaban Namibiya Hage Geingob ya yi jinyar makonni da cutar corona. A tsakiyar watan Yuni ne kuma shugaban kabilar Herero Vekuil Rukoro ya ce ga garinku biyo bayan kamuwa da COVID,

Mali | UN Minusma Mission | Soldaten der Bundeswehr
Majalisar Jamus ta amince sojojin kasar su ci gaba da aiki a MaliHoto: Alexander Koerner/Getty Images

Jaridu sun yi tsokaci kan aikin sojojin Jamus a kasar Mali

"Lokaci ya yi na yada kwallon mongoro" da haka ne jaridar der Freitag ta bude sharhin da ta yi a kan gazawar tawagar sojin da ke fafutukar samar da zaman lafiya a yankin Sahel. Kamata ya yi rundunar sojin Jamus ta janye daga Mali kamar yadda ta yi a Afganistan. A cewar jaridar dai, rauni da wasu sojojin Bundeswehr suka ji a 'yan kwanakin nan, ba shi ne karon farko da sojin Jamus din suka jikkata ba. Masu lura da lamuran yau da kullum na ci gaba da dasa ayar tambaya dangane da tasirinsu.

Shekaru biyun da suka gabata ne dai sojojin Jamus da ke aiki a karkashin rundunar sojojin hadakar MDD ta MINUSMA suka rasa rayukansu a hadarin jirgi mai saukar ungulu a Mali. Tuni dai kwararru suka yi gargadi dangane da yiwuwar sake samun sabuwar Afganistan a yankin Sahel.

Shin mene ne dalilin kai sojojin Jamus a yankin? Gwamnatin Merkel kan gabatar da dalilai guda uku: Yaki da tarzoma, gudunmawa wajen kare gwamnatin Mali da makwabtanta, kuma wajibi ne a dakatar da matsalar gudun hijira. Da haka ne mafi rinjayen 'yan majlisar Bundestag ke tsawaita wa'adin sojojin da fakewar kwalliya na biyan kudin sabulu, amma kuma a zahiri sabanin haka ne.

A shekara ta 2013 ne Faransa ta shiga wannan yaki, inda aka cimma nasarar fatattakar mayakan jihadi da ke rike da madafan ikon yankin arewacin Mali. Daga bisani ne MDD ta karbi ikon kula da dorewar zaman lafiya. Sai dai mayakan sun sauya salon yaki, inda suka sake kafa rundunar fadada hare harensu zuwa yankin Sahel baki daya, wanda ya sa Faransa martani da rundunar Barkhane. Sai dai yanzu hare haren sun kara ta'azzara.

Äthiopien Tigray-Krise | Soldaten TPLF
Hoto: Ben Curtis/AP/picture alliance

 Zaman lafiya ya kasa samuwa a yankin Tigray a cewar jaridun Jamus

Ita kuwa jaridar Der Tagesspiegel yankin kahon Afirka ta dosa a kan rikicin yankin Tigray. Jaridar ta ce, a yanayi na bazata, gwamnatin Ethiopiya ta ayyana tsagaita wuta, sai dai 'yan tawayen Tigray na muradin ci gaba da yaki. Bayan abun da ke zaman raguwar sojojin gwamnati a yaki basasar Ethiopiya a yankin Tigray, a ranar Litinin ce, dakarun tawayen suka kwace  madafan ikon babban birnin yankin watau Mekele. Gabanin hakan dai an gwabza kazamin fada tsakaninsu da dakarun gwamnati, inda dubban mayakan Ethiopiyan suka tsere. Watanni takwas kenan birnin yake karkashin ikon mayakan na gwamnati.

Da yammacin Litinin ne dai, gwamanatin Addis Ababa ta sanar da tsagaita wuta ita kadai a yakin. Hakan na da nufin bai wa manoma damar share gonakinsu kana kungiyoyin kasa da kasa zasu samu damar kai agaji Tigray, a cewar sanarwa da ta fito daga gwamnatin framinista Abiy Ahmed.