1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar kungiyar tarayyar Turai EU.

Mohammad Nasiru AwalAugust 23, 2004
https://p.dw.com/p/Bvh7
Shugaban hukumar kungiyar EU, Jose Manuel Barroso
Shugaban hukumar kungiyar EU, Jose Manuel BarrosoHoto: AP

A cikin shekaru kalilan da suka wuce, batutuwa guda biyu suka fi daukar hankali a cikin KTT EU. Na farko shine shirin shigar da karin kasashe 10 a cikinta, na biyun kuma shine muhawwara game da kundin tsarin mulkinta. In ban da wadannan babu wani abin fararta rai da ya auku cikin kungiyar EU a baya-bayan nan. Hasali ma wasu manyan kasashen kungiyar kamar tarayyar Jamus, suna fama ne da matsalolin marasa aikin yi.

A taron da suka yi a birnin Lisbon shekaru 4 da suka wuce shugabannin kasashe da na gwamnatocin EU sun kuduri aniyar mayar da wannan kungiya ta zama ja-gaba a karfin tattalin arzikin duniya kafin shekara ta 2010. Ko da yake wannan wani buri ne da ya cancanci yabo, amma har yanzu ba wani canji na ku zo ku gani da aka yi bisa cimma wannan burin da aka sa gaba. Hasali ma tattalin arzikin kasashen Turai sai yi baya yake maimakon gaba.

Kwararrun masana sun ce muddin ana son a samu wani ci-gaba a harkar zuba jari to ya zama wajibi a yi gyara a manufar ba da tallafi ga manoma, domin kudaden tallafin na cin kaso mafi yawa a kasafin kudin kungiyar EU. Kuma idan ba´a dauki matakan yin sauyi cikin gaggawa ba, kungiyar EU zata rushe, musamman bayan an fara baiwa sabbin membobinta kudaden tallafin.

To sai dai ba kudaden tallafin da ake ba manoman ne kadai ke bukatar canji a cikin sabuwar hukumar karkashin Jose Manuel Barroso ba, dole ne a samu hadin kai tsakaninshi da majalisar ministocin EU, don aiwatar da dokokin daidaita kasafin kudin kasashen kungiyar, wanda Faransa da Jamus suka karya, sakamakon matsalolin gibin kasafin kudi da suke fuskanta. Dole ne kuma a dauki sahihan matakai game da kasafin kudin kungiyar a gaba.

Ba abin mamaki ba ne kuwa da mista Barroso ya rage yawan ma´aikatun kudi da na tattalin arziki, sannan shi da kanshi zai rika kula da yarjejeniyar Lisbon dangane da inganta harkokin tattalin arzikin kungiyar.

Tambayar da ake yi yanzu ita ce wai mai zai faru ga sabbin kasashen da ke fatan shiga cikin kungiyar EU a badi? Ko shakka babu za´a bukace su da su daidaita tattalin arzikinsu. Hazakalika duk wani mataki da sabuwar hukumar zata dauka zai dogara ne da irin kamun luden sabon kwamishinan kula da aikin fadada kungiyar, Siim Kallas. Babban kalubalen da zai fuskanta a kuwa shine idan ba´a samu wani ci-gaban tattalin arziki nan ba da dadewa ba a cikin kungiyar ta EU, to za´a fuskanci adawa mai tsanani a shirye-shiryen daukar sabbin kasashe cikin kungiyar.