Makomar Jam'iyyun adawa a Najeriya
October 11, 2024Jam'iyar adawa ta PDP alal misali, shugabanni biyu ne Ilia Damagun da Ahmed Yayari ke ikirarin halastaccen shugabancin jam'iyyar a mataki tarayya. A yayin kuma da a jam‘iyyar labour Nenadi Usman ke gwada kwanji da Julius Abure. Can ma cikin gidan NNPP akwai ikirarin Abba tsaya da kafarka. Duka a cikin guguwar da ke kara tada hankali a ciki da wajen jam'iyyun.
Komawa zuwa ga Rabbana cikin batun adawar ko kuma farkon Karshen PDP cikin fagen siyasa, In har tsohuwa tana magagin mutuwa, ita ma NNPP da ke zaman kwaila a siyasar ba ta tsira ba a guguwar rigingimun da ke cikin fagen siyasar.
Can cikin Kano, jiha guda da ke ikon jam'iyyar dai, kai yana rabe a tsakanin masu neman tawaye bisa tsarin da ke gudana a jihar, da kuma masu tunanin dorawa bisa jagorancin Rabi'u Musa kwankwaso. Hashim Suleman shi ne shugaban jam'iyyar NNPP a jihar, kuma yace shedanci ne kokarin raba Abba da mai gidansa na siyasa a jihar. To sai dai in har tarbiyar na nuna alamun karanci cikin fagen siyasa a kasar, sabbabin rigingimun na zaman barazana mai girma a fagen siyasar kasar.
Duk da cewar dai a karon farko an yi nasarar kaiwa shekaru 25 kan tsarin dimukuradiyya a kasar, rigingimun siyasar dauri ne dai a fadar Farfesa Kamilu Sani Fage da ke zaman kwarrare a batun siyasa suka kai ga zuwa jana'izar tsarin cikin kasar can baya.
Duk da cewar dai sun fi karkata zuwa ga adawa ita kanta APC dake takama da mulkin tarayyar najeriyar dai ba ta tsira ba cikin jerin rigingimun da suka kalli kasa kiran taron majalisar zartarwar jam'iyyar na kasa sama da shekara guda. Ko a wannan ranar an dakatar da wasu jiga jigan jam'iyyar da suka hada da minista a jihar Bayelsa