Makomar jam′iyyar PDP bayan Bamanga Tukur | Siyasa | DW | 17.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Makomar jam'iyyar PDP bayan Bamanga Tukur

Akwai alamun a cimma nasarar kawo ƙarshen rikicin siysar da jam'iyyar mai mulki ta kwashe dogon lokaci ta na fama da shi a Najeriya.

Cikin ƙiftawar ido da bisimilla ne dai aka kai ga kawo ƙarshen gagwarmayar ikon da ta mamaye jami'iyyar PDP mai mulki a Najeriyar. To sai dai kuma ba tare da ɓata lokaci ba ne kuma ido ke neman buɗewa a cikin jami'yyar daga dukkan alamun ke fatan sake zawarcin 'yan biyar na gwamnonin dama ya'yan majlisun ƙasar biyu da ke iƙirarin raba gari da gidan na wadata bisa kallamai dama aiyyukan Bamanga.

Tunanin manazarta a kan makomar jam'iyyar ta PDP

Ba mamaki wasun manyan ƙusoshin jam'iyyar da suka fice su sake komawa a fadar Christy Tafiɗa Silas da ke zaman 'yar majalisar ƙolin jam'iyyar abin da ka iya buɗe wani sabon babi ga jam'iyyar. To sai dai kuma tun ba'a kai ga ko'ina ba dai murnar ta fara neman komawa ciki ga ya'yan PDP waɗanda sannu a hankali ke ganewa da sauran tafiya a ɓurin sake haɗewar jam'iyyar tare da maidata mafi tasiri cikin ƙasar. Babu dai gwamna ɗaya tilo a cikin biyar da ya nuna alamar komawa gidan wadatar gadon, haka ma kusan dukkanin 'yan majalisar wakilan ƙasar 37 da su ka yi ƙaura suka bar jam'iyyar a faɗar Hon Bashir Babbale da ke zaman ɗaya a ciknsu ba su da imanin komawa da nufin taka rawa a cikin harkokin jam'yyar.

Babban ɓuri jam'iyyar a nan gaba bayan wannan al'amari

Duk da cewar dai babban ɓurin jam'iyyar a gaba shi ne na tabbatar da zaman lafiya,daga dukkan alamu dai babban rikici a gaban jam'iyyar na zaman rabuwar kawunan 'yan jam'yyar wajen tabbatar da shugabancin PDP na gaba. To sai dai kuma a faɗar Bello sabo Abdulkadir da ke zaman jigo a cikin 'yan rikicin PDP dai ɓurin na zaman neman tabbatar da cimma shugaban ƙasar da 'yan PDP ke yi wa kallon kanwa uwar gamin ɗaukacin rikicin da ya mamaye jam'iyyar na tsawon kusan shekara guda. Abun jira a gani dai na zaman mafita ga jam'iyyar da ke fatan kawo ƙarshen rigingimun da ke barazana ga ɗorewar tasirin jam'iyyar a zaɓukan ƙasar a nan gaba.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto haɗe da rahoton da wakilinmu na Yola Muntaqa Ahiwa ya aiko mana

Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Abdourahamane Hassane

Sauti da bidiyo akan labarin