Makomar bukatar Turkiya ta shiga tarayyar Turai | Labarai | DW | 21.06.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Makomar bukatar Turkiya ta shiga tarayyar Turai

Bore a Turkiya ya janyo sabani a tsakanin Turai a kan bukatar shigar da ita cikin kungiyar.

Ana samun tsaiko wajen kara kusantar kasar Turkiya da kungiyar Tarayyar Turai. A wani zama da suka yi a birnin Brussels na kasar Beljiyam, wakilan kungiyar sun kasa cimma matsaya game da bukatar bude sabon babi a tattaunawar da ake yi domin karbar Turkiyar a cikin kungiyar. Wakilan sun ba da sanarwar cewa kasashen Jamus da Holland sun nuna rashin amincewa da hakan. Ita dai kasar ta Turkiya tana shan suka ne game da matakin ba sani ba sabo da ta dauka akan masu zanga-zanga. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kira matakin 'yan sandan Turkiyar da ya halaka mutane hudu ya kuma raunata wasu dubu 7 da 500 tamkar mataki mai tsauri. Zanga-zangar dai ta taso ne bayan da gwamnatin Turkiya ta sanar da shirinta na yin gine-gine a wurin shakatawar nan na Gezi da ke birnin Istanbul. To sai dai ministan Turkiyar dake kula da harkokin kungiyar Tarayar Turai, Egeman Bagis yayi wa Merkel kashedi game da yin amfani da bukatar hadewar Turkiyar da kungiyar Tarayyar Turai a matsayin makaminta na yakin neman zabe.

Mawallafiya : Halima Balaraba Abbas
Edita : Zainab Mohammed Abubakar