Makauniya ta ci makwafin lambar Nobel | Zamantakewa | DW | 27.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Makauniya ta ci makwafin lambar Nobel

Wata matashiyar lauya kana makauniya 'yar kasar Habasha da ke gwagwarmayar kare nakasassu tana cikin mutane hudu da suka samu lambar kyauta makwafin ta Nobel ta zaman lafiya.

Mutane hudu da suka samu wannan lamba ta kyauta da aka kirkiro domin kara karfin gwiwa ga mutane da suke fafutuka da sadaukar da rayuwarsu, domin ganin al'umma na samun rayuwa mai inganci. Mutane hudu da suka samu wannan kyauta ta shekara ta 2017, sun hada da Robert Bilott lauya mai fafutukar kare muhalli a Amirka, da Colin Gonsalves mai kare marasa galihu a Indiya, kana akwai Khadija Ismayilova wadda take kwarmata bayanai domin tozarta wadanda ke cin hanci da rashawa a kasar Azerbaijan.

Sai kuma Yetnebersh Nigussie makauniya kuma lauya 'yar kasar Habasha wadda take kare rayuwar nakasassu. Nigussie ta samu nasarori duk da irin rashin fahimta da wasu ke da ita bisa nakasa a kasashe masu tasowa na Afirka kamar Habasha:

Äthiopien Gewinnerin des alternativen Nobelpreises, Yetnebersh Nigussie (privat)

Nigussie 'yar fafutika a yanayin nishadi

"Galibin mutanen Habasha suna danganta nakasa da wani sabo da wani daga cikin iyalai ya aikata. Amma abin da ya saka nake ganin makantata a matsayin wata dama shi ne, saboda galibi mutane a kauyenmu ba su halarci makaranta ba lokacin da aka haife ni."

Ta kara da cewa ba ta dora alhakin makantarta kan wani saboda rashin ilimi da ya mamaye kauyen da aka haifeta, sannan Nigussie ta kara da cewa galibin kawayenta sun yi aure tun suna da shekaru 10 zuwa 11 da haihuwa ita kadai ta rage wadda ta zurfafa ilimi. A cewarta da tana gani zai yi wuya ta yi zurfin karatu zuwa matakin zama lauya, domin da ta yi auren wuri, kuma babu yadda za ta taimaka wa al'umma kamar yadda yanzu take yi.

Äthiopien Gewinnerin des alternativen Nobelpreises, Yetnebersh Nigussie (Joel Sheakoski)

Nigussie 'yar fafutika kuma lauya a tsakiya

Kana wani babban abin da take takama da shi na zama kafa cibiyar inganta rayuwar nakasassu. Ita dai Nigussie tana aiki a matsayin lauya da wata kungiyar kare hakkin dan Adam da ke kasar Habasha, saboda yaki da nuna kyama, wannan 'yar gwagwarmayar ta yi fice a matsayin matashiya daga kasashe masu tasowa kana makauniya.

Galibin kasashen Afirka sun saka hannu a kudirin tabbatar da dakile nuna wariya ga masu nakasa, abin da Nigussie ta yaba bisa nasarar da ake samu, amma ta ce har yanzu da sauran aiki:

Yetnebersh Nigussie 'yar shekaru 35 da haihuwa tana alfahari da mijinta gami da 'ya'ya biyu da take da su.