1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makami mai linzami kirar Rasha ya sauka a Poland

Binta Aliyu Zurmi
November 16, 2022

Mahukunta a Poland sun tabbatar da saukar makami mai linzami a wani kauye da ke kusa da iyakar kasar da Ukraine, wanda ya yi sanadiyar rayukan mutane biyu.

https://p.dw.com/p/4JaLg
Andrzej Duda
Hoto: Michal Dyjuk/AP Photo/picture alliance

Shugaba Andrzey Duda ya ce makamin samfurin kasar Rasha ne, sai dai ya kara da cewar har a zuwa wannan lokacin babu kwakwarar shaida akan wanda ya harbo shi. Amma na fara bincike.

Harin da ya sauka a kan guda daga cikin kasashen mambobin kungiyar tsaro ta NATO ya assasa taron gagawa, wanda shugaban Amirka Joe Biden ya shugabanta, ya kuma tabbatar da cewar zai iya janyo mumunar ramuwar gayya daga kungiyar.

Rasha dai tuni ta fidda bayani da ke musanta zargin harba wannan makami da Ukraine ke yi mata, mahukuntan na Poland na shirin kara tsaurara tsaro a sararin samaniyar su tun bayan wannan hari da suka ce mai cike da barazana.