Makaman Najeriya na fadawa hannun Boko Haram | Labarai | DW | 13.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Makaman Najeriya na fadawa hannun Boko Haram

Kungiyar Cluster Munition Coalition mai yaki da yaduwar haramtattun makaman yaki ta ce nau'in wasu makamai da Boko Haram ke kai hari da su sun fito ne daga runbun ajiyar kayan yaki na Najeriya.

Wata kungiya mai yaki da yaduwar haramtaccin makamai a duniya mai suna Cluster Munition Coalition ta tabbatar da cewa Kungiyar Boko Haram na yin amfani da wasu kananan bama bamai da ainahi suka fito daga rumbun ajiyar makaman Najeriya wajen kaddamar da hare-haren bama-baman da su ke kaiwa kan ayarin motoci ko a kasuwanni da masallatai na kasar.

Kungiyar Cluster Munition Coalition ta ce hotunan bama -baman da hedikwatar sojojin Najeriya ta wallafa kan shafinta na Tweeter na nunar da cewa bama- baman da sojin Najeriyar suka gano na sanfarin BLG-66 ne kirar kasar Faransa , kuma ana kyautata zaton wannan makami ya shigo hannun Boko Haram din daga runbun ajiyar kayan yaki na kasar ta Najeriya

Kakakin babbar hedikwatar sojojin Najeriyar Rabe Abubacar shima dai ya tabbatar a baya bayan nan da cewa sun gano irin wadannan makamai a wata maboyar makaman 'yan Boko Haram da suka bamkado a cikin jihar Adamawa da ke a yankin Arewa maso Gabashin kasar.