Majalisar wakilan Najeriya na zargin ɓangaren zartarwa da kutse | Siyasa | DW | 03.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Majalisar wakilan Najeriya na zargin ɓangaren zartarwa da kutse

'yan majalisar wakilai sun ce ɓangaren zartarwa na yi mu su shisshigi, inda suke zarginsu da kwaskware dokar naɗa hafsoshin soja ba tare da gabatar da shi a gaban majalisar ba

A yanayin da ke zama barazana ga dimokraɗiyyar Najeriya, majalisar wakilan ƙasar ta yi zargin cewa a asirce ɓangaren zartaswa ya yi gyaran fuska ga dokar da ta shafi harkokin hukumomin tsaro na sojan Najeriya, abin da ya saɓawa tsarin mulkin ƙasar. Wane hatsari wannan ke da shi ga tsarin dimoƙraɗiyyar ƙasar?.

To sannu a hankali dai ana ƙara bankado abubuwan da ake ganin an ɓoyewa majalisar da ma sauran al'ummar ƙasar a game da dokar da ta ba da ikon naɗa hafsoshin rundunonin sojan Najeriyar

Zargin majalisar wakilai

Majalisar wakilan ƙasar da ta gano cewa ɓangaren zartaswan ya yiwa wannan doka gyaran fuska a asirce ba tare da tuntuɓar majalisar ba kamar yadda dokar ƙasa ta tanada, ta yi gargaɗin hatsarin da ke tattare da kaucewa ginshiƙai da sharuɗɗan dimokraɗiyya a kan wannan batu.

Hon Ibrahim Tukur El-Sudi shi ne ya gabatar da wannan ƙuduri a gaban majalisar kuma ya bayyana man abinda ya gano a canjin da suke zargin ɓangaren zartswar sun yi.

***Für mögliche Ergänzungen der Karte, wie z.B. andere Sprachen, zusätzliche Orte oder Markierungskreuz, wenden Sie sich bitte an infografik@dw-world.de (-2566), Außerhalb der Bürozeiten an bilder@dw-world.de (-2555).*** DW-Grafik: Per Sander 2011_03_10_Laender_Prio_A_B

"An bawa shugaban ƙasa cikakken ikon ya naɗa waɗanan hafsoshin soja ko na ƙasa ko na ruwa ko na sama kuma tillas ne ya kawo majalisa domin a tanatance, amma abin mamaki sai aka yiwa wanan doka gyaran fuska, maimakon hafsan tsaro, sai suka sa ministan tsaro wanda ba tilas ne a ce yana da ƙwarewa ta fanin tsaro ba, sa'anan kuma sai suka cire wannan sashin da y ce tillas sai sun je majalisar ƙasa''.

Hukuncin da kotu ta yanke kan wannan batu

Rikita-rikitar da ke cikin wannan al'amari dai ta ƙara bayyana ne a fili bayan hukuncin da babban kotun da ke Abuja ta zartas wanda ke cewa naɗin da shugaban Najeriya ya yi wa hafsoshin sojan ƙasar ba tare da neman amincewar majalisar datawa ba ya saɓawa tsarin mulkin Najeriyar kuma haramtacce ne.

Sanin irin matsayin da tsarin mulkin dimokraɗiyya ya baiwa 'yan majalisar dokoki da su ne ke da ikon kafawa da ma yi wa dokokin gyaran fuska bisa tsarin dimokraɗiyya ba wai ɓangaren zartaswa ba ya sanya nuna damuwa musamman yadda Najeriya ke da dokoki barkatai a kundin tsarin mulkinta, ko wane hatsari ke tattare da wannan mataki da bangaren zastawar ya dauka? Dr Usman Mohammed shi ne shugaban ƙungiyar nazarin 'yan majalisu a Afrika, kuma ma masanin kimiyyan siyasa ne da ke Abuja.

"Hatsarin shi ne su waɗanan majalisu da kuma ɓangaren shugaban ƙasa kowa na duban kowa ne yadda ba wanda zai fi ɗan uwansa karfi, to duk lokacin da aka ce ɓangaren zartaswa ta tashi ta yi gyara, wannan wuce wuri ne, kankamba ne kuma ba a yi duk duniya. To ya dace yanzu su tsaya su ga wane gyara ne ɓanagren shugaban ƙasa suka yi suka wuce wuri su yi tir da shi su mayar da dokarsu yadda yake da, sanan kuma su tsaya a kan wannan dokar da suka yi''.

Matsaloli tsakanin majalisar da ɓangaren zartarwa a baya

A lokutan baya dai an sha kai ruwa rana tsakanin majalisar dokokin Najeriyar da ɓangaren shugaban ƙasa a kan kauce ƙa'ida, da ma yin hawan ƙawara a kan tsarin mulkin da shi ne ya hallatawa kowane sashi ikon gudanar da aiyyukansa.

To sai dai ba kasafai ake jin inda ta kaya ba. To amma Hon Ibrahim Tukur El-Sudi ya ce ƙadammar da binciken da suka yi a kan wannan lamari zai tabbatar da daukan matakai da zasu samar da mafita daga irin wannan matsala.

"Ladabtar da duk wanda yake da hannu a cikin wanan shishigi zai kasance ɗaya daga cikin ainihin abubuwan da zai sa nan gaba ba wani wanda zai yi sha'awar ya yi gyaran fuska a tsarin mulki ba tare da ya tuntubi majalisa ba''.

A duk lokacin da aka samu kuskure da wasu kan danganta shi da cewa da sani a kan yi hawan ƙawara ga ginshikan dimokraɗiyya a Najeriya 'yan siyasa kan yi saurin kare kansu da cewa dimokraɗiyyar ƙasar rarrafe take yi, abin da ke sa talakawa da sauran mabiya tambaya shin yaushe ne dimokraɗiyyar zata gama rarrafe har ta fara takawa domin baiwa talaka dammar fatan kaiwa ga tudun na tsira?

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Pinaɗo Abdu Waba

Sauti da bidiyo akan labarin