Majalisar Jamus ta fusata kan kutsen Intanet | Labarai | DW | 01.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Jamus ta fusata kan kutsen Intanet

Hukumomin Jamus sun ce su na sane da masu kutsen Intanet, sai dai sun jinkirta ne domin samun damar cafke su.

Hukumomin Jamus sun ce su na sane da masu kutsen Intanet, sai dai sun jinkirta ne domin samun damar cafke su, amma lamarin ya fusata yan majalisar dokoki wadanda sai a kafofin yada labarai suka san abun da ake ciki.

'Yan majalisun dokokin sun bukaci sanin dalilin da ya sa gwamnati ba ta sanar da su ba.

Kwamitin majalisar dokokin Jamus mai kula da tattara bayanan sirri yace akwai yiwuwar kutsen da aka yi wa harkar sadarwa Intanet na gwamnatin yana ci gaba da gudana.

Shugaban kwamitin Armin Schuster yace tabbas an yiwa wasu sassan gwamnati kutse ta Intanet amma ba tare da gasgata rahoton kafofin yada labarai ba cewa masu satar kutse ta yanar gizo na Rasha sune ke da alhakin lamarin.

Ministan cikin gida na Jamus Thomas de Maiziere yace kutsen wani hari ne aka tsara shi cikin kwarewa tsawon lokaci, sai dai yace an shawo kan lamarin.