1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Duniya ta amince a yaki fyade

Gazali Abdou Tasawa
April 24, 2019

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kudirin yaki da fyade a lokutan yaki da Jamus ta gabatar donn magance matsalar da ta kazanta a kasashen da ake yaki.

https://p.dw.com/p/3HJHh
USA New York - UN Sicherheitsrat zu sexueller Gewalt
Hoto: Getty Images/D. Angerer

Da kuri'u 13 ne dai Kwamitin sulhun na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kudirin a yayin da kasashen Rasha da China suka yi rowar kuri'unsu. Sai dai mutanen da suka samu kyautar zaman lafiya ta Nobel ta 2018 Denis Mukwege dan kasar Kwango da Yazidie Nadia Murad sun bayyana rashin jin dadinsu dangane da barazanar amfani da kujerar naki da kasar Amirka ta yi, a lokacin muhawarar, sun kuma  bayyana bukatar ganin an kare hakkin mutanen da aka yi wa fyaden a lokutan yakin.

Kasar Amirka dai ta gitta sharadin janye maganar izinin zubar da ciki kafin ta amince da kudirin, a yayin da kasashen Rasha da China da Amirkar suka kuma bukaci cire matakin saukaka hanyoyin iya gurfanar da mutanen da ake zargi da aikata fyade da kudirin ya tanada. Lamarin da ake ganin ya rage karfin kudirin wanda ainahi Jamus din ta gabatar da shi ne da nufin rage kaifin wannan matsala ta ayyukan fyaden da ake aikatawa a lokutan yakin a kasashen duniya da dama.