Majalisar dokokin Rasha ta amice da wata doka a kan ƙungiyoyi | Labarai | DW | 19.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar dokokin Rasha ta amice da wata doka a kan ƙungiyoyi

Dokar dai za ta ba da izini ga gwamnatin na haramta kafuwar wasu ƙungiyoyi na waje masu zaman kansu a Rasha.

Majalisar dokokin Rasha ta amince da wata doka wacce aka kwashe dogon lokaci ana yin ka ce na ce a kanta. Dokar dai za ta bai wa gwamnatin damar haramta kafuwar wasu ƙungiyoyin na ƙasashen waje a Rashar wanda gwamnatin ke ƙemarsu.

Majalisar ta amince da gaggarumin rinjaye da dokar a karatu na uku kafin a nan gaba shugaban Vladimir Putin ya rataɓa hannu a kan ta.