Majalisar dokokin Najeriya ta sa hukumar EFCC a gaba | Siyasa | DW | 01.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Majalisar dokokin Najeriya ta sa hukumar EFCC a gaba

Majalisar dokokin Najeriya ta buƙaci gudanar da bincike kan duk kaddarorin da hukumar yaƙi da cin hanci ta EFCC, ta ƙwato tun da aka kafa ta.

national assembly.jpg

A wani abun dake iya kama hanyar ɓallo rikici game da makomar yaƙin cin hancin Tarrayar Najeriya, majalisar wakilan ƙasar ta umarci ƙaddamar da bincike kan kaddarori da kuɗaɗen da hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci a Tarrayar Najeriya ta ƙwace a cikin shekaru kusan 10 da suka gabata.

A baya dai sun kai ga fyaɗar yaro da kuma jefa tsoro a zuƙatan manyan cikin gidan Tarayyar Najeriya. Sun kuma karɓi kaddarori da kuɗaɗen da suke jin a sace a ƙoƙarin ƙasar na yaƙar annobar cin hanci. To sai dai kuma daga dukkan alamu tana shirin ji a jiki ga hukumar yaƙi da halsata haramun da yanzu haka ke shirin amsa tambayar ina ajiyar kaka da kakkani.

Wani zaman majalisar wakilan Najeriyar dai ya umarci ƙaddamar da bincike kan ɗaukacin kuɗaɗe dama kaddarorin jama'ar da ta kwace a cikin yakin na shekaru kusan 10 da suka gabata. Kaddarorin kuma da suka kai na kusan naira miliyan zambar dubu kusan biyu ko kuma rabin kasafin kudin kasar na shekara guda.

Nigeria's former anti-corruption czar Nuhu Ribadu addresses a primary convention in Lagos, Nigeria, on Friday, Jan. 14, 2011. Ribadu who won international acclaim for seeking charges against members of the oil-rich nation's political elite, was chosen Friday as the presidential candidate of the country's strongest opposition party. Ribadu's entry into the race comes hours after the nation's ruling People's Democratic Party overwhelmingly endorsed President Goodluck Jonathan in a primary election decided just before dawn on Friday. (AP Photo/Sunday Alamba)

Nuhu Ribadu, shugaban EFCC na farko.

Halin da kadarrorin da hukumar ta karɓo suke.

Manyan manyan gidaje da hotel hotel da ragowar kadarrori da kudade ne dai yanzu haka ke hannun hukumar amma kuma babu wanda ya san halin da suke cikin balle sanin abun yi da kudin. Abun kuma da ya tada hankulan yan majilasar da tuni wasunsu ke zargin da damansu sun bi shannun sarki

a baya dai irin wadannan kudade da aka karbo a wajen tsoffafin shugabannin mulkin sojan kasar ta nigeria sun kare ne cikin aljihunan masu ruwa da tsaki da harkokin kasar na baya.

Abun kuma da a cewar Hon Auwal dahiru Azare dake zaman dan majalisar wakilan daga Bauchi ya tilasta su neman bin ba'asin dukiyar alummar kasar.

Anti-Korruptionsbehörde begleiten Dimedschi Bankole, ehemaliger Sprecher des nigerianischen Parlament im weissen Gewand, zur Gerichtverhandlung in Abuja wegen Korruptionsvorwurf. Foto: Ubale Musa, 08.06.2011, Abuja / Nigeria

Jami'an EFCC da tsohon shugaban majalisar wakilai, Bankole.

Matsayin cin hanci da rashawa a Najeriya

To sai dai kuma batun na barawo a zaune ya karba hannun na tsaye ko kuma wasa da hankalin yan kasa dai sabuwar fitilar dake kokarin haska aiyyukan EFCC dai na zuwa ne a daidai lokacin da wasu gwamnonin kasar ke korafin amfani da hukumar da nufin gallaza musu cikin gwagwarmayar siyasar da ta fara daukar zafi yanzu haka.

Hukumar dai ce fadar ta Aso rock a baya ta shuna domin jefa kowa layi a bukatar tabbatar da dorewar mulkin PDP a ikin tarrayar nigeriar a baya. Abin da kuma yanzu haka ya fara jefa tsoro a zukatar yan kasar kan yiwuwar maimaicin rawaa sabuwar siyasar kasar ta Najeriya.

Ana ma dai kallon shi kansa matakin majalisar a zaman wani kokarin rage kaifin efcc da ma kila cire hakorin cizo tun ma kafun lokacin fara haushin nata.

Auwalu Musa Rafsanjani dai na zaman shugaban kungiyar Transparency in Nigeria dake kula da yakin kasar na cin hanci daga bayan fage, kuma a cewar sa duk wani kokari na jefa hukumar cikin siyasa to kuwa zai kare ne da kara illa a cikin yakin.

Sama da Dallar Amurka miliyan dubu 500 ne dai suka bi ruwa atsakanin jamian gwamantin kasar ta nigeria da yan korensu a daya daga cikin tarihin cin hanci mafi girma a duniya baki daya.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Saleh Umar Saleh

Sauti da bidiyo akan labarin