Majalisar dokokin Libiya ta fara yin zamanta cikin ruɗani | Labarai | DW | 04.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar dokokin Libiya ta fara yin zamanta cikin ruɗani

An buɗe zaman taron ne a cikin saɓanin ra'ayoyi tsakanin masu kaifin kishin addini da kuma jam'iyyun siyasar masu kishin ƙasa.

Majalisar dokokin Libiya ta soma yin zamanta na farko a garin Tobruk da ke da nisan kilomita 1500 daga gabashin birnin Tripoli don gujewa yaƙin da ake yi.

Tsakanin ƙungiyoyin mayaƙa waɗanda ke ɗauke da makamai kusan makonnin da dama, wanda a cikin ɗarurruwan jama'a suka rasa rayukansu. Masu kishin addinin na garin Misarata da ke a yammancin ƙasar, sun ƙauracewa bikin buɗe zaman taron wanda suka ce ya saɓama kudin tsarin mulkin ƙasar.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasir Auwal