Majalisar dokokin Jamus za ta yi muhawara | Labarai | DW | 07.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar dokokin Jamus za ta yi muhawara

Majalisar dokokin ta Jamus watau Bundestag za ta tattauna batun kasafin kudin kasar na shekara ta 2017.

An shirya shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel za ta yi jawabi a lokacin bude taron.Wanda ya zo kwanaki biyu kacal bayan mummunar kayan da jam'iyyar da ke yin mulki watau CDU ta sha a zaben jihohin da aka yi ran Lahadin da ta gabata a jihar Mecklemburg-Vorpommern.

Masu aiko da rahotnnin sun ce da alama za a tafka muhawara mai zafi a lokaci zaman taron da za a kwashe kwanaki hudu ana tattauna sabon kasafin kudin kasar.