Majalisar Dinkin Duniya za ta amince da tura dakaru Mali | Labarai | DW | 29.11.2012
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Dinkin Duniya za ta amince da tura dakaru Mali

Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-moon, ya ce Kwamitin Sulhu zai amince da tura dakaru afkawa masu kaifin kishin Islama na Mali.

Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-moon, ya bayyana cewa Kwamitin Sulhu zai amince da tura dakaru, domin afkawa masu kaifin kishin Islama na ƙasar Mali amma ƙasashen Afirka za su ɗauki ɗawainiyar kaɗaɗen da za a kashe.

Ban ya ce Kwamitin Sulhun ya nemi shiri mai ƙarfi na tura dakaru, tare da kayan aiki, wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ba ita za ta bayar da kuɗin tafiyarwa ba. Ya ƙara da cewa babu bayani kan jagorancin dakarun, sama musu horo, da inda za a samo kuɗaɗen aikin, waɗanda abubuwa masu mahimmaci. Amma ƙasashen Afirka ba su yi bayani akai ba.

Cikin watan Maris Azbinawa masu alaƙa da ƙungiyar al-Qaeda sun kwace yankin arewacin ƙasar Mali, sakamakon juyin mulkin da sojoji su ka yi a Bamako babban birnin ƙasar. Ƙasasehn yankin yammacin Afirka sun nemi amfani da ƙarfi muddun tattaunwa ta ci tura.

Zai yi wuya a ƙaddamar da hari kan yankin arewacin na Mali kafin watan Satumba na shekara mai zuwa, saboda ruwan sama da ake samu daga watan Juni zuwa Agusta, kamar yadda masu tsara dabarun yaƙi na Afrika su ka bayyana. Ana sa ran amincewa da shirin cikin watan Disamba mai zuwa.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Halima Balaraba Abbas

 • Kwanan wata 29.11.2012
 • Muhimman kalmomi Mali
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/16sJ9
 • Kwanan wata 29.11.2012
 • Muhimman kalmomi Mali
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/16sJ9