Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da Trump | Labarai | DW | 12.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da Trump

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana kalaman shugaban kasar Amirka Donald Trump a kan kasashen Haiti da Afirka da abin kunya bayan da ya danganta kasashen da taron tsintsiya ba shara.

A ranar Alhamis shugaba Trump ya ce bai ga dalilin da Amirka za ta karbi 'yan gudun hijira daga kasashen Haiti da Afirka ba wadanda ya kira da taron tsintsiya ba shara, a maimakon haka gara kasar ta karbi 'yan gudun hijira daga kasar Norway wadanda ya bayyana da cewar mafiya yawan su farar fata ne.

Wannan furuci da Trump ya yi kan kasashen Haiti da Afirka ya fusata 'yan siyasa daga Jam'iyyar Democrats da kuma Republican a fadin kasar inda su ka yi zarginsa da rura wutar wariyar launin fata.

Rupert Colville ya kara da cewar bai dace shugaban kasa kamar Amirka ya bude kofar Kin jini da wariyar launin fata bata .Daga nan sai ya ce irin wadannan kalamai na Trump sunyi hannun riga da kokarin shimfida zaman lafiya da duniya take yi tun bayan yakin duniya na biyu.