Majalisar Dinkin Duniya ta tura dakarunta a Bangui | Labarai | DW | 15.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Dinkin Duniya ta tura dakarunta a Bangui

Dakarun Majalisar Dinkin Duniya sun karbi aiki daga hannun dakarun Tarayyar Afirka na Misca, da suka jima suna ayyukan tsaro a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Hakan ta faru ne yayin wani kasaitaccen buki da aka shirya a sansanin sojojin kiyaye zaman lafiyar da ke filin jirgin saman birnin Bangui.

A wurin wannan buki, babban jami'in kwantar da tarzoma na Majalisar Dinkin Duniya Hervé Ladsous, ya mika hular sojan Majalisar mai ruwan bula ga babban kwamandan kiyaye zaman lafiya na Majalisar ta Dinkin Duniya da ke Jamhuriyar Afirka MINUSCA Janar Martin Chomu Tumenta dan kasar Kamarun. A baya shi ne ya jagoranci dakarun tarayyar Afirka na Misca. Bukin ya kuma samu halartar dakarun Shugabar kasar ta rikon kwarya Catherine Samba Panza, da kuma wakilan dakarun kasar Faransa na Sangaris da na Tarayyar Turai na Eufor.