Majalisar Dinkin Duniya ta kammala ziyarar ′yan gudun hijira a Najeriya | Siyasa | DW | 22.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Majalisar Dinkin Duniya ta kammala ziyarar 'yan gudun hijira a Najeriya

Wata tawagar masu sa ido ta Majalisar Dinkin Duniya da ta kammala ziyarar matsugunan wadanda rikicin Boko Haram ya rutsa da su inda ta nemi Najeriya ta kara kulawa.

Flüchtlingslager in Bama, Nigeria

'Yan gudun hijira a Bama

Tawagar ta wakilai uku dai ta share tsawon kwanaki biyar tana rangadin matsugunai daban-daban na wadanda suke gudun rikicin a jihohin Borno da Yobe da Adamawa, da kuma cibiyar sauyin hallayar 'yan taádar na Boko Haram da ke a Abuja, kafin daga bisani su kira wani taron manema labarai da a cikinsa 'yan tawagar suka ce har yanzu da sauran aiki a kokari na kyautata 'yanci da rayuwa ta wadanda rikicin ya rutsa da su.

Duk da cewar akwai matakai a bangaren mahukunta na kasar na samar da ginshikai na sake inganta rayuwa da mayar da su cikin al'umma, har yanzu akwai jerin matsaloli kama na basu kariya tare da kyautata rayuwa tsakanin mata da yaran da ke rayuwa a matsugunan.

Ravina Shamdasani

Ravina Shamdasani mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya kan hakkin bil Adama

Maud DeBoer Buquicchio da ke zaman daya a cikin masu sa idon ya ce akwai bukatar daukar karin matakai a bangaren gwamnatin tarraya da jihohin da abun ya shafa domin tabbatar da kare aikata lafukan cin zarafin mata da yara a cikin matsugunan.

"Wata damuwar da muke da ita ita ce ta damar samun adalci. Tabbatar da hukunta duk wadanda suka take hakkin mata da yara ya zama wajibi, musamman ma wadanda suka tilasta su auren dole ko kuma yi musu fyade".

Duk da cewar dai kasar ta yi ikirarin samun ci gaba daga kokari na kyutata rayuwa zuwa na sake hadasu da sauran al'umma tawagar dai ta ce kasar ta Najeriya na bukatar inganta cibiyoyin ilimi da lafiya a matsayin hanyar kai wa ga tabbatar da dorewar zaman lafiya a yankin na Arewa maso Gabas a cewar Dainius Puras wanda shi ma ya taka rawa a sa'idon.

Nigeria Flüchtlinge wegen der Offensive gegen Boko Haram

Yara a sansanin 'yan gudun hijira a Geidam Yobe

"Kamar yadda duk muka sani harkokin ilimi da lafiya su ne suka fi shan wahala a hannun Boko Haram. An kashe ko kuma sace malaman lafiya da ke samar da dama ta lafiya da rayuwa mai amfani, haka kuma malamai da ke ilimantar da al'ummar yankin , haka kuma asibitoci da makarantu an konesu ko kuma lalatawa, yana da muhimmanci a tabbatar da sake bude makarantu domin samar da damar ilimi musamman na mata ba tare da tsoro ba".

Rahoton har ila yau ya tabo 'yan mata 'yan makaranta ta Chibok da ke cika shekaru biyu da bata a watan Afrilun da ke tafe, sannan kuma ya nemi gwamnatin kasar da yin cikkaken bayyanin irin hobbasan da take da nufin ceto yaran.

Sauti da bidiyo akan labarin