1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Majalisar Dinkin Duniya ta goyi bayan kafa kasar Falasdinu

Mouhamadou Awal Balarabe
September 12, 2025

kuri'u 142 sun goyi bayan kudirin samar da zaman lafiya mai dorewa a Gabas ta Tsakiya da zai shata kafa kasar Falasdinu, yayin da 10 suka nuna adawa da shirin ciki har da Amurka, su kuma 12 suka yi rowar kuri'arsu.

https://p.dw.com/p/50Q40
Akasarin kasashen duniya sun amince da shata hanyar da za ta kai ga kafa kasar Falasdinu
Akasarin kasashen duniya sun amince da shata hanyar da za ta kai ga kafa kasar FalasdinuHoto: ANGELA WEISS/AFP/Getty Images

Duk da adawar da Isra'ila da Amurka suka nuna, babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya amince da shirin farfado da tsarin samar da kasashe biyu na Isra'ila da Falasdinu, tare da mayar da kungiyar Hamas saniwar ware.

A yayin da Isra'Ila ke sukar hukumomin duniya saboda zargin gaza yin Allah wadai da harin da kungiyar Hamas ta kai mata a Oktoban 2023, kuri'u 142 sun goyi bayan kudirin samar da zaman lafiya mai dorewa a Gabas ta Tsakiya, yayin da 10 suka nuna adawa ciki har da Amurka, su kuma 12 suka yi rowar kuri'arsu.

Karin bayani: Ko duniya za ta bar Isra'ila ta mamaye Gaza?

Wannn mataki na zuwa ne gabanin babban taron Majalisar Dinkin Duniya wanda Faransa da Saudiyya za su jagoranta a ranar 22 ga watan Satumba, inda Emmanuel Macron ya yi alkawarin amincewa da yankin Falasdinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta.

Jakadan Falasdinawa a MDD Riyad Mansour ya mayar da martani inda ya yi kira ga Isra'ila da ta mutunta matakin da aka dauka ba tare da nuna wa MDD turjiya ba. A nata bangaren, Isra'ila ta yi watsi da kudurin, wanda ta kira shi da abin kunya da ke karfafa waHamas gwiwar yakar ta.