1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar dattijan Amirka ta amince da shirin tsige Trump

February 10, 2021

Tsohon shugaban Amirka Donald Trump zai gurfana domin ci gaba da shari'ar tsige shi bayan da majalisar dattijai ta yi watsi da da'awar lauyoyinsa cewa bai halasta a tsige shi ba saboda ya riga ya bar karagar mulki.

https://p.dw.com/p/3p8u7
USA Impeachment-Prozess gegen Trump
Hoto: U.S. Senate TV/REUTERS

'Yan majalisa 56 suka kada kuriar amincewa yayin da 44 kuma suka ki amincewa da kudirin tsige tshon shugaba Trump. Ko da yake yawancin 'yan majalisar sun kada kuriar ce da muradun jam'iyyunsu, 'yan majalisa shidda na jam'iyyar Republican sun yi hannun riga da jam'iyyarsu inda suka kada kuri'ar amincewa da shirin tsige tshohon shugaban kasar Doanld Trump.

Sai dai har yanzu 'yan Democrats na da jan aiki a gaba na iya shawo kan karin 'yan majalisu 11 na Republican kafin su sami rinjaye don tsige tshohon shugaban. Trump yana fuskantar tuhuma ce kwaya daya na tunzura jama'a domin bijirewa gwamnati wanda 'yan Democrats suka ce Trump ne ya assasa gangamin. Sai dai Lauyan Trump Bruce Castro yace batun tsige Trump ba shi da wani tasiri saboda ya riga ya sauka daga karagar mulki.