Majalisar dattawan Najeriya ta karbi sunayen ministoci | Labarai | DW | 30.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar dattawan Najeriya ta karbi sunayen ministoci

Shugaban Tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya mika sunayen ministoci da yake son nadawa ga majalisar dokokin kasar domin amincewarsu.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban majalisar dattawan kasar Bukola Saraki wanda ya sanar a shafinsa na Twitter ya bayyana cewa an damka masa sunayen ministocin da Shugaba Muhammadu Buhari ke son nadawa a mukamai daban-daban. In baya ga ministan albarkatun man fetur kawo yanzu tsahon watannin biyar da rantsar da sabuwar gwamnatin Buhari babu wata ma'aikata da aka san wanda zai jagoranta.

Shi dai Shugaba Buhari ya sanar da cewa shi ne da kansa zai jagoranci ma'aikatar kula da albarkatun man fetur wadda cin hanci da almundahana da kudaden al'umma ya yi wa dabai-bayi. Har yanzu dai al'ummar Najeriya na dakon sanin sunayen mutanen da Buhari ya mika domin jagorantar ma'aikatun kasar.